Gwamna Aminu Bello Masari ya mika wannan bukata yau ta hannun Jakadan Kasar a Najeriya Moustapha Awwad a ofishin jakadancin kasar dake Abuja.

Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa bunkasa harkar noma, samar da Ilmi da kuma kiwon lafiya sune manyan kudurorin gwamnatin shi tun lokacin da ya karbi ragamar mulkin a shekarar 2015. Kuma bakin gwargwado, an fara shinfida harsashi mai kyau don cimma wannan kuduri har an fara ganin nasara, kwatsam sai matsalar tsaro tayi kamarin da ba a zata ba. Hakan yasa kuma tilas gwamnati ta karkata wajen samar da tsaro ga al’umma.

Gwamnan ya kara da cewa, neman yin hadin guiwar da kasar Misra ya samo asali ne ganin yadda kasar tayi zarra a cikin kasashen duniya ta wadannan bangarori, dadin dadawa kuma a shekarun baya an yi irin wannan da kasar ta bangaren Noma kuma an ga alfanun shi.

Gwamna Masari ya shaida ma Jakadan cewa al’ummar jihar Katsina bamu da wata sana’a da ta wuce noma, kuma ga shi Allah Ya albarkace mu da kasar noma kuma da jajirtattun mutane, musamman matasa, da suka rike ta. Ta bangaren Ilmi kuwa, jihar tayi suna wajen Ilimin addinin Musulunci tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka. Haka kuma ba a bar ta a baya ba wajen Ilimin boko, wanda ko a yanzu haka gwamnati tayi tsarin samar da Ilmin farko ga yara na tsawon shekaru tara kuma tasa shi ya zama tilas domin yaran su shirya ma zurfafa Ilmin su zuwa manyan makarantu.

A nashi jawabin, Jakada Awwad ya sha alwashin gayyato masu zuba jari zuwa jihar Katsina domin tattaunawa da gwamnati domin fito da bangarori da kuma yadda za su zuba jari domin amfanin kasashen biyu.

Ya kuma bayyana cewa akwai masana da za su shigo daga Jami’ar Azhar dake Al-Kahira (Cairo) domin gabatar da wani taro kan Ilmin Kimiyya da na addini, sai kuma ya bukaci gwamnatin jiha da ta tura wakilanta domin ganawa da wadannan masana na Jami’ar Azhar domin fayyacewa tare da fito da bangarori da kuma irin daukin da Jihar ke bukata.

Jakada Moustapha Awwad ya bada shawarar gwamnati ta bada makarantu guda biyu wadanda za a hallanta ma wadannan masana domin su tsara masu manhaja ta koyarwa tare da samar da littattafan koyarwa da ake bukata domin dora yara bisa ingantacciyar hanyar koyon kwasakwasan Kimiyya da na addinin Islama.

Ya kara da cewa, ofishin jakadancin a shirye yake domin hada jami’an ma’aikatun gona da na Ilmi na jihar da takwarorin su na Misra domin tattaunawa da fito da irin daukin da za a kawo ma jihar.

Ta bangaren kiwon lafiya kuwa, Moustapha Awwad ya bayyana cewa gwamnatin kasar tasu tana daukar nauyin gina kananan dakunan shan magani ga al’ummomin da suke cikin sako da kuma samar da motocin kula da marasa lafiya na tafi da gidan ka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here