Advert
Home Sashen Hausa GWAMNATIN JIHAR KATSINA TA BADA UMARNIN RUFE DUKKAN WURAREN HAWA MOTA WADANDA...

GWAMNATIN JIHAR KATSINA TA BADA UMARNIN RUFE DUKKAN WURAREN HAWA MOTA WADANDA SUKE BA’AKAN KA’IDA BA A FADIN JIHAR.

 

A cikin ci gaba tare da bin diddigi game da bin hanyoyin da zasu magance matsalar Tsaro, Majalisar Zartarwa ta Jiha ta yi taronta na yau da kullun na 5 da aka gudanar ranar Laraba 8 ga Satumba, 2021 ta yi bitar tanade-tanaden Dokar kuma ta amince da haka:

a) Rufe dukkan tashoshin mota wadanda suke ba akan ka’ida ba a dukkan kananan hukumomin 34 da babban birnin jihar nan da nan;

b) Majalisar ta kuma ba da umarnin duk motocin kasuwanci gami da manyan motocin bas Su mayar da ayyukansu nan take zuwa tashoshin da aka amince dasu domin hawan mota.

C) Majalisar ta kuma amince da tilasta amfani da rigunan jaket masu nuna abinda ke cikinsu ( Reflective jacket) ga duk Masu Babur na Kasuwanci a fadin Jihar.

Ma’aikatar Jiha ta Ayyuka, Gidaje da Sufuri ta bada Samfurin Jaket ɗin Da Ya dace.

Wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar ta ce an umarci kwamishinonin kananan hukumomi da masarautu da ayyuka, gidaje da sufuri da dukkan hukumomin tsaro don tabbatar da bin ka’idar dokar.

Abdullahi Aliyu Yar’adua

Daraktan yada labarai na SGS.

Muhammad Garba MG

Ya fassara da Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: