Home Sashen Hausa GWAMNATIN JAHAR KATSINA TA KAMMALA AIKIN GININ SABUWAR MASARAUTAR GALADIMAN KATSINA HAKIMIN...

GWAMNATIN JAHAR KATSINA TA KAMMALA AIKIN GININ SABUWAR MASARAUTAR GALADIMAN KATSINA HAKIMIN MALUMFASHI.

GWAMNATIN JAHAR KATSINA TA KAMMALA AIKIN GININ SABUWAR MASARAUTAR GALADIMAN KATSINA HAKIMIN MALUMFASHI.

Shugaban Kamfanin Gine Gine Na (Muntasrab Global Concept Nig LTD) Engr Muntari Sagir Malumfashi, ya mika makullen ginnin katafariyar masautar Galadiman katsina hakimin Malumfashi, Wanda Gwamnatin jahar katsina ta Gina a karkashin offishin Kwamishinan Kananan hukumomi da masarautu da Al’adu.

Shagaban Karamar hukumar Malumfashi, Alhaji Abdulrahaman Marafa ne ya amshi aikin a madadin Karamar hukumar Malumfashi.

A cikin jawabin shi, Engr Muntari sagir, yayi godiya ga masaruta, Karamar hukuma da Kuma Al’ummar Kofar fada, bisa ga had’in kai, da Kuma goyan baya da suka bada a lokacin da yake Gudanar da aikin.

Haka nan Engr Muntari, yayi kira ga masaruta da duk wani Abu na gyara in ya taso ayi mashi magana indai mafi karfin shi ba, zai gyara ba sai anje ga hukuma ba.

A cikin jawabin shi Shugaban Karamar hukumar Malumfashi, yayi bayanin irin aiyukan da Engr Muntari sagir yayi wanda basu cikin aikin da aka bashi kwangila domin kishin Karamar hukumar Malumfashi.

Galadiman katsina. hakimin Malumfashi. Tsohon mai shiria Sadik Abdullahi Mahuta, yayi godiya bisa ga wannan aikin da akayi ma masaruta, mussaman ga Mai Girma Gwamnan Jahar katsina,Rt. Hon. Aminu Bello Masari, da Kuma Shugaban Karamar hukumar Malumfashi, da Shugaban Kamfanin Gine Gine Na Muntasrab.

A inda ya Kara godiya ga Engr Muntari sagir, bisa ga Abubuwan da ya Kara da yawa da Aljihun shi.

Yayi mashi addu,ar fatan Alkhairi sannan ya yaba da za’ben da Gwamna Masari yayi na jan Engr Muntari a jikin shi, inda yace lallai Gwamna Masari, baiyi za’ben tumun dare ba.

Daga karshe Galadima katsina hakimin Malumfashi, yayi Addu’ar AlLah ya jikan Galadima Nasiru, da sauran Hakimin da akayi a wannan masaruta ta Karamar hukumar Malumfashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Full Police Statement; on 1/2020

FULL POLICE STATEMENT ; ON 1/2020 ARREST OF THREE MEMBERS OF NOTORIOUS SYNDICATE OF BANDITS/KIDNAPPERS AND RECOVERY OF RANSOM MONEY, THE SUM THREE MILLION AND...

Hukumar Tsaron farin kaya ta DSS ta gayyaci shugaban masu safarar kayan abinci zuwa kudu

Yanzu yanzu: Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gayyaci Shugaban masu safarar kayan Abinci bisa dalilin rufe hanya da hana kai kayan Abinci...

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya yi gargadin...
%d bloggers like this: