A yau Juma’a 06 ga Zulhijjah, 1441 ne gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Ganduje ta kame Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara, ta kuma gabatar da shi gaban kotu, wacce ta ba da izinin a tsare shi har zuwa ranar 28 ga Yulin 2021 don ci gaba da sauraron karar.

Wannan labarin ya fito ne a wata takardar manema labarai da Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Mal. Muhammad Garba ya sa wa hannu aka raba wa manema labarai da yammacin yau din nan.

Shi dai Malamin an gabatar da shi ne a yau Kotun Upper Sharia Court, Kofar Kudu, inda Alkali Ibrahim Sarki Yola, ke alkalanci.

Bayan karanto masa tuhume-tuhume da suka hada da yin batanci ga Annabi Muhammadu, sai Alkalin ya dage sauraron shari’ar zuwa 28 ga Yuli, 2021.

Amma Shehin Malamin zai zauna a hannun ‘yansanda har sai ranar Litinin da za a tura shi gidan yari.

Ga matanin Takardar manema labarai din da Turanci:

Press Release

Court charges Abduljabbar for blasphemy, incitement, remands in correctional centre

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, the Kano-based Islamic cleric famous for his controversial religious commentaries and statements that are regarded as statements mortifying the companions and sacrilegious to the Holy Prophet Muhammad (S.A.W) has been charged to court for blasphemy.

A statement issued by the commissioner for information, Malam Muhammad Garba indicated that the development followed the receipt of the First Information Report from the police by the Office of the Attorney General and commissioner for justice which prepared charges against the cleric.

Abduljabbar was subsequently arraigned on Friday, July 16 before an Upper Sharia Court Judge, Kofar Kudu, Alkali Ibrahim Sarki Yola, where the charges that included blasphemy, incitement, and sundry offences were mentioned.

The statement added that after the court sitting, it adjourned the case to July 28, while the scholar would remain under police custody until Monday when he would be sent to prison till the adjourned date.

MALAM MUHAMMAD GARBA

Hon. Commissioner for Information, Kano State

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here