Gwamnatin Filato ta tabbatar da wawashe wuraren ajiyar kayan abinci a jihar

Jos

Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da rahotannin wawashe ɗakunan ajiyar kayan tallafin annobar korona da dubban mutane suka yi a Jos, babban birnin jihar.

Sai dai ta ce ba gaskiya ba ne batun da ake yaɗawa cewa ɓoye kayayyakin ta yi, tana mai cewa zanga-zangar EndSars ce ta tilasta dakatar da raba wa mabuƙata.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai Dan Manjang ya fitar a yau Asabar, an yashe wuraren ajiyar abinci na Jos da Bukuru ranar Asabar 24 ga Oktoba.

An ga dubban mutane a wasu bidiyo daban-daban da suka karaɗe shafukan sada zumunta suna ɗibar kayayyaki daga wurin ajiyar abinci a Jos.

Social embed from twitter

“Gwamnati ta yi tur da wannan aiki sannan tana jaddada cewa ba ɓoye su ta yi ba,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa a ranar 16 ga Oktoba Ministar Ma’aikatar Agaji, Cigaban Al’umma da Kare Afkuwar Bala’i, Sadiya Umar Farouk, da Ministar Mata Dame Paullen Tallen, suka kai kayan tare da ma’aikatan da za su raba su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here