Gwamnatin Buhari ta soki rahoton da aka fitar kan rashawa a Najeriya

Buhari

Mai magana da yawun fadar Mal. Garba Shehu ya ce ba a yi musu adalci ba a rahotan, domin duk wanda yasan ƙasar da abubuwan da ke faruwa yasan gwamntinsu na kokari.

Rahoton Transparency ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta biyu cikin ƙasashen da aka fi tafka rashawa a yammacin Afirka a shekara ta 2020.

Wannan na nuna cewa rashawar da ake tafkawa a ƙasar ya karu kamar yadda rahotanta ke nunawa cikin shekaru biyu.

Sai dai Garba Shehu ya yi watsi da hujojin da ƙungiyar ta yi amfani da su wajen kafa hujja da tattara bayananta.

Ya kuma shaida irin nasarar da ya ce suna samu a yaƙi da rashawa da kuɗaɗen da aka ƙwato da matsayin da gwamnatinsu ke kai a yanzu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here