Gwamnatin Amurka ta zartar da hukuncin kisa kan wata mace

..

Gwamnatin Amurka ta zartar da hukuncin kisa kan Lisa Montgomery, wadda ita ce mace ɗaya tilo da ke jiran a zartar mata da hukuncin kisa a Amurka – bayan samun ta da laifin aikata kisan kai.

An yi wa Montgomery allurar guba a wani gidan yari da ke Terre Haute a jihar Indiana ta Amurka.

Kafin mutuwarta, wannan lamarin ya ja hankalin duniya ganin cewa lauyoyinta sun dage kan cewa tana da matsalar ƙwaƙwalwa, haka kuma sun ce ta fuskanci cin zarafi matuƙa da tana yarinya.

Montgomery, mai shekara 52, ta shaƙe wata mai ciki da igiya, inda ta yi amfani da wuƙa ta farka mata ciki ta ciro jaririnta a jihar Missouri a 2004.

Hakan ya sa mahaifiyar jaririn, Bobbie Jo Stinnett mai shekara 23 ta yi ta zubar da jini har ta mutu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here