Advert
Home Sashen Hausa Gwamnatin Aminu Masari Zata ɗauki ƴansandan Unguwanni(Community Policing)

Gwamnatin Aminu Masari Zata ɗauki ƴansandan Unguwanni(Community Policing)

Domin karfafa wa jami’an tsaro guiwa wajen samarwa da inganta tsaro cikin jihar nan, Gwamnatin Jiha a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta kafa kwamitin da zai tsara yadda za a rika kula da tsaro a matakin unguwanni (Community Policing).

Haka kuma ba da jimawa ba, shirye shirye za su kankama na daukar matasa daga kananan hukumomin mu talatin da hudu wadanda za su gudanar da wannan aiki.

Kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya ce za ta basu horo da kuma kayan aikin da suka dace domin tabbatar da an samar da tsaro a fadin jihar nan.

Muna kuma aiki a kan wata doka da za ta kafa kwamitocin kula da tsaro a matakin gunduma (Hakimi) da kuma yanki (Magaji), wanda za a dauko wakilan wadannan kwamitoci daga cikin masu ruwa da tsaki na wadannan yankuna.

Wannan doka za ta fitar da rawar da kowane bangare na al’umma zai taka wajen wannan aiki wanda zai maganin kalubalen tsaro da muke fuskanta.

Da yardar Allah, muna da kwarin guiwa tare da kyautata zaton wadannan matakan za su kawo sassafcin da zai ba al’ummar mu kwanciyar hankalin da za suci gaba da al’amurran su na yau da kullum cikin natsuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

TSAKANINA DA GWAMNATIN KATSINA(kashi na uku)

  Kabir sadiq (Dan Abu) A baya na tsaya inda mukayi waya da ADC kuma yaje ya gaya wa maigirma gwamna yadda abun yake, shi Bafarawa...

“My political career ends with the governorship of Rt. Hon. Aminu Bello Masari”…..Muntari Lawal

The opening caption above is his replay to us when we proposed to him to aspire for governorship race in 2019. His closing remarks...

A 39-year-old man, Ahmed Abdulmumini, has been arrested by the Katsina State Police Command for alleged cyber-stalking.

According to the police, Abdulmumini’s arrest followed a complaint by Governor Aminu Masari’s Special Adviser on Domestic Affairs, Alhaji Ibrahim Umar. Umar allegedly told the...

Tsohon Ministan Noma Abba Sayyadi Ruma ya Rasu a Birnin London

Da Dumi-Dumi: Tsohon Ministan Noma, Alhaji Abba Sayyadi Ruma Ya rasu a Birnin Landan INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN Allah yayima Alhaji Abba Sayyadi Ruma rasuwa...
%d bloggers like this: