Gwamnati ta yi wa ASUU tayin naira biliyan 65

Copyright: @FKEYAMO
Gwamnatin Najeriya ta yi tayin naira biliyan 65 ga ƙungiyar malaman Jami’o’i (ASUU) na kuɗaɗen alawus ɗin malaman da kuma farfaɗo da jami’o’in.
Ministan ƙwadago da ayyukan yi, Dr Chris Ngige ne ya bayyana matakin na gwamnati ga ƙungiyar malaman a ganawar da suka yi ranar Juma’a.
Ministan ya bayyana tattaunawar a matsayin mai fa’ida yayin da gwamnati ta yi tunanin sauya matsayi kan jayayyar da take da da ƙungiyar malaman wanda ya hana ɗalibai karatu tsawon watanni.
Ministan ya ce gwamnati ta yi tayin biliyan 15 daga cikin kuɗaɗen matsayin na farfaɗo da jami’o’in, bayan biliyan 20 da gwamnati ta biya tun da farko.