#GaskiyarLamarinNijeriya @Ko kunsaniNG

Ko kun san cewa, a cikin shekaru biyar kacal Gwamnatin Shugaba Buhari, ta hannun Bankin Samar da Gidaje na Nijeriya (FMBN), ta gina gidaje guda 10,519 ga ma’aikata daga cikin 30,915 da bankin ya gina tun daga kafa shi shekaru 25 da suka shuɗe?

Wannan ya gwada cewa, Gwamnatin Shugaba Buhari ce ta gina kimanin kashi ɗaya bisa uku na yawan gidajen da bankin ya gina, amma ta gina ne a kashi ɗaya bisa biyar na shekarun bankin tun daga kafuwarsa, domin kuwa gwamnatocin baya sun iya gina gidaje guda 20,435 ne kawai a aƙalla cikin shekaru 20.

Gidajen dai sun kasance masu sauƙin kuɗi ne a dukkan faɗin ƙasar, waɗanda suka kama daga masu ɗaki ɗaya zuwa masu ɗakuna uku, kamar yadda Hukumar NDPHC ta bayyana a ranar 4 ga Nuwamba, 2021.

Idan dai za a iya tunawa, a shekara ta 2018 Gwamnatin Tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa, kamar NLC, TUC da NECA, suka cimma yarjejeniyar samar da bashin gidaje masu sauƙin kuɗi ga ma’aikata a ƙarƙashin shirin samar da gidaje na ƙasa, inda nan da nan gwamnatin ta cire Naira Biliyan Takwas ta gina gidaje guda 1,400 kan farashi mai rahusa na Naira Miliyan Huɗu ga gidaje masu ɗakuna ɗaya da Naira Miliyan Takwas ga masu ɗakuna uku.

A kashi na biyu na shirin kuwa, Gwamnatin Shugaba Buhari ta ware zunzurutun kuɗi Naira Biliyan 17 ne, don samar da ƙarin gidaje 2,700, duk a cikin ƙoƙarin da ta ke yi wajen ganin ta inganta rayuwar al’umma da ma’aikatan ƙasar tare da samar da aikin yi, don tsamo ‘yan Nijeriya daga ƙangin talauci!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here