Advert
Home Sashen Hausa GWAMNATI SHOULD BE CAREFUL, KAR TAYI RESTOCKING YAN TA'ADDA A KATSINA ...

GWAMNATI SHOULD BE CAREFUL, KAR TAYI RESTOCKING YAN TA’ADDA A KATSINA Daga Al Amin Batsari

GWAMNATI SHOULD BE CAREFUL, KAR TAYI RESTOCKING YAN TA’ADDA A KATSINA
Daga Al Amin Batsari

Jiya naga a TV Maigirma Gwamna ya karbi wasu tubabbun shuwagabannin yan ta’adda. Sun kawo AK 47 guda 10, wai sun (Gaji da abinda suke yi na ta’addanci) sun zo a yahe masu, sun tuba. 🤔

To yanzu naji, sunzo sun tuba. Sun gaji dda abinda suke yi, to wa zai yahe masu? Shin Maigirma Gwamna zai yahe abinda ba shi aka zalunta ba, bai ma san wanda aka zalunta ba, ko kuwa al’ummar da aka zalunta ne suke da hakkin yafewa?

Idan Gwamna ya yafe zaluncin da ba shi akayi mawa ba, shi kuma wa zai yafe mashi? Allah dai baya yafe hakkin wani akan wani.

Na biyu, wake da tabbas na Makaman da aka kawo masu kyau ne ba lallatattu bane? Sun kawo ne kawai don yaudarar da suka saba?

Maigirma Gwamna ga Shawara

Na farko dai mu kara jin tsoron Allah. Mu Sani babu wanda ke da hakkin yahe abinda aka yiwa iyayen mu da kankannin mu Sai mu, kuma bamu yahe ba.

Na biyu, Duk wanda yazo yace ya tuba, to Gwamnati ta rike shi, a koma wurin wanda aka zalunta a tambaye su, “Tsohon Dan Ta’adda wane, wanda ya jagoranci kashe ku, da yi ma matanku fydae, da sace maku dukiya. Yau yayi nadama yace ya Bari. Amma yana neman ku yafe mashi. Kun yafe? In bamu yahe ba, a kai shi kotu ayi mashi hukunci.

Na uku, Maigirma Gwamna, dukkan mutanen nan, jahilci ne musabbabin abinda suke yi, don in ba jahili ba, babu wanda zai yiwa mace fyade saman santa, gaban yayan ta. In ba jahili ba, babu Mai iya kunnawa kaza wuta da ranta har ta mutu, bare ace mutum. To maganin wannan jahilci shine ilimi. A bi hanyar data dace, shuwagabanni su dora su wanda suka tuba bisa hanyar ilimi, hanyar Sharadin Tuba da Allah (S. W. A) ya gindaya, wadda Hadith Manzon Allah (S. A. W) yazo da ita.

Na hudu, Maigirma Gwamna, a guji yiwa Yan ta’addar hasafi da suna sun Tuba. Ba a gudun ma su dauko bindigu da sun lalace, tunda dai ba sanin bindigar nan kuka yi ba, kuma ba cewa za ayi in anzo gabanka a halba don a tabbatar mai kyau bace. Don haka suna Iya kawo maku unserviceable bindigu, su saida maku, su amshi kudin su koma daji su sawo sabbi, daga nan su cigaba daga inda aka tsaya. Abinda ya faru kenan lokacin Sasancin da ya gabata. Don saida suka zabe bidigun masu kyau, suka baku rubabbi. Aka basu kudi suka sawo babura masu gudun tsiya masu karfi, da bindigu. Daga lokacin yan ta’addar dake birnin Gwari, kusa da Faskari, suna Iya zuwa Batsari ko Jibia suyi ta’addanci hankali kwance tunda sun samu abun Hawa.

Na biyar Sir, criminality dai ya zama way of life na mutanen nan. Basu san wata Hulda ba sai da criminals yan uwansu. Basu san wani aiki ba na neman abinci sai ta’addanci. Sir, yanzu tubar su na bukatar canza masu hanyar rayuwar su (Rehabilitation). Irin wannan ana yinshi ta hanyar creating camp, a canza masu tunani, a basu ilimi, su zauna wurin na watanni yadda zasu fito suna mutanen kirki, da basu sha’awar komawa waccen rayuwar. Wa ke da alhakin hakan? Dole sai an taimaka ma su sun canza hanyar rayuwar su. Amma yanzu bahillace da ake gani bakauye, bindigar shi ta lalace, babu abin neman kudi, sai ya kawo a ce ya Tuba, a gode mashi, a bashi kudi yayi cefane da tsarabar birni ga iyali, ya kuma sawo wata bindigar Sabuwa.

Na shida Sir, yaya zaka yarda da bahillace da yake daji, da makamin, yana neman kudi, ya dauko wasu daga makamin ya kawo maka, ka Saya da sunan ya Tuba, don kawai yanzu yaga kokarin da Gwamnati take yi da Jami’an tsaro, da al’ummar Gari ya Sanya Kidnapping din ma da suke yi ana basu kudi yanzu babu riba, da sunyi Kidnapping 1 ko 2 sai an kama su. Sai a dade ba a samu sa a ba. Saboda addua da wayar da kai da Gwamnatin keyi. Amma Kuma karshe a kawo maka makamin ka amshi makamin ka bashi kudin da yake nema ya koma daji? Babu dubara Sam anan.

Gaskia sai anyi hattara. Yanzu dai Jami’an tsaro sunyi kokarin rage hanyar da mutanen nan suke samun kudi da makamai matukar yadda ko a haka, a ci nasara. Gwamnati tayi kokari matuka ta karfafawa Jami’an tsaro, al’umma kuma suna basu goyon baya. Yanzu option daya ne ya rage, shine suzo wurin ka. Don Allah kar ayi restocking din su. Kar a maida mu ruwa.

Inshaa Allah mu dai wannan shawara ce muka bada, kuma zamu cigaba da wannan fadakarwar ga al’ummar mu don kowa ya fahinci yanzu halin da ake ciki. Mun dai bada Shawara, za kuma mu fadiwa al’umma halin da ake ciki. In sun ga yan bindiga sun samu sabbin makamai, to Gwamnati ce ta basu kudi. Shikenan!

Allah ya sa mu dace.
Daga shafin Al Amin Batsari na Facebook

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

YANZU-YANZU: Darakta-Janar na Inuwar Gwamnonin APC ya ajiye muƙamin sa

Darakta-Janar na Inuwar Gwamnonin APC, Salihu Lukman ya ajiye muƙamin sa. Jaridar Vanguard ta rawaito cewa ajiye muƙamin na sa na da nasaba da rikicin...

THE M.K.O. ABIOLA NATIONAL STADIUM IN ABUJA HAS BEEN SUCCESSFULLY REHABILITATED!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/257296063153585/

RASHIN TSARO: Attajiri Aminu Dantata ya fashe da kuka…

Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya Ta Yi Silar Zubar Da Hawayen Aminu Dantata Yayin Gudanar Da Taro Hamshaƙin ɗan kasuwar nan Alhaji Aminu Alhassan Dantata...

Har yanzu: Gwamna Masari na Alhinin Rasuwars Kwamishinan Kimiyya Rabe Nasir

Gwamna Aminu Bello Masari ya kara bayyana rasuwar Dokta Rabe Nasir a matsayin babban rashi duba da yadda yake da jajircewa tare da sadaukarwa...

Katsina lawyer in court over alleged cheating,forgery, impersonation

A Funtua based Company in Katsina state, NAK International Merchant has dragged a Lawyer, Barrister Mahdi Sa'idu to court over alleged cheating, forgery and...