Home Sashen Hausa Gwamnati Kaɗai Ba Za Ta Iya Wadata Jami’o’in Najeriya Da Kuɗi Ba—...

Gwamnati Kaɗai Ba Za Ta Iya Wadata Jami’o’in Najeriya Da Kuɗi Ba— Buhari

Gwamnati Kaɗai Ba Za Ta Iya Wadata Jami’o’in Najeriya Da Kuɗi Ba— Buhari

Zaharaddeen mziag katsina city news

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ita kaɗai ba za ta iya wadata jami’o’in Najeriya da kuɗi ba.

Shugaba Buhari ya ce dole kamfanoni masu zaman kansu su shigo harkar wadata jami’o’in Najeriya da kuɗaɗe saboda nauyin ya yi wa Gwamnatin Tarayya yawa.

Da yake jawabi a Bikin Yaye Ɗalibai da Kuma Bikin Cika Shekara 72 Da Kafuwa na Jami’ar Ibadan ranar Talata, Shugaban Ƙasar ya ce ya kamata jami’o’i su jawo hankalin kamfanoni masu zaman kansu.

Shugaba Buhari ya samu walilcin Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa, NUC, Farfesa Abubakar Rasheed.

Ya ƙalubalanci jami’o’i da su fito da shirye-shirye da za su taimaka wa gwamnatinsa wajen rage talauci da kuma inganta ɓangaren lafiya.

“Ya zama dole a lura da cewa gwamnati ita kaɗai ba za ta iya ɗaukar tarin nauyin ilimi ba. Dole kamfanoni masu zaman kansu su shigo wajen samar da ilimi mai inganci a Najeriya.

“Ina zaton jami’o’in za su mayar da kansu ababen sha’awa a wajen kamfanoni masu zaman kansu, su bada ma’anar aikace-aikacensu su kuma fito da wata hikima ta hanyar tsara shirye-shirye da za su taimaki gwamnati wajen rage talauci da inganta ɓangaren lafiya”, in ji shi.

Shugaba Buhari ya kuma gargaɗi shugabannin hukumomin gudanarwa na jami’o’in Najeriya da su daina yin katsalandan waje nada shugabannin jami’o’i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: