Gwamnan Tambuwal da Sarkin Musulmi sun ziyarci Zamfara

Gwamnan jihar Sakkwato Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal CFR tare da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Saad Abubakar sun ziyarci Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle domin jajanta masa sace daliban da aka yi a Jangebe.

Gwamnan ya nuna alhini tare da kaduwa kan abinda ya samu takwaransa na jihar Zamfara. Ya kuma sha alwashin taimakawa jihar wajen ganin al’amura sun daidaita tare da yin duk mai yuwuwa wajen ganin an sako wadannan dalibai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here