Da yammacin yau, Gwamna Aminu Bello Masari ya kai ziyarar duba wasu ayyuka guda da suke da dumbin muhimmanci ga wannan jiha da al’ummar ta.

Wadannan ayyuka su ne sabon ginin Ofishin hukumar tara kudin shiga ta jiha (Board of Internal Revenue) wanda ake kusa da kammalawa, sai kuma ofishin hukumar kula Malaman Makarantu ta jiha (Teachers’ Service Board).

Bayan kammala wannan ziyara, Gwamna Aminu Masari ya nuna gamsuwar shi da yadda ayyukan biyu suke tafiya.

Shi sabon ofishin na hukumar kula da Malaman Makarantu TSB, ana gina shi karkashin wani shiri na hada ka tsakanin gwamnatin jiya da ‘yan kasuwa masu zaman kan su, a inda sanannen kamfanin nan na GREEN HOUSE ya dauki nauyin gina ma hukumar sabon ofishi na zamani a cikin farfajiyar sakatariyar gwamnatin jiha, daura da Ma’aikatar lafiya, ita kuma gwamnati za ta hallanta wa kamfanin gine ginen da hukumar take zaune a ciki yanzu, wanda suke kan titin IBB daura da GREEN HOUSE din, da zarar wancan aiki ya kammala.

A yayin wannan ziyara, Gwamnan ya sami rakiyar Mataimakin shi Alhaji Mannir Yakubu da wasu daga cikin wakilan Majalisar zartaswa ta jiha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here