Advert
Home Sashen Hausa GWAMNAN KATSINA YA KAI ZIYARA AIKIN GIDAJE 185 DA YAKE GINAWA

GWAMNAN KATSINA YA KAI ZIYARA AIKIN GIDAJE 185 DA YAKE GINAWA

GWAMNAN KATSINA YA KAI ZIYARA AIKIN GIDAJE 185 DA YAKE GINAWA

A bisa kudurin Gwamnatin Jiha nakammala duk ayyukan da take kai, a yau, Gwamna Aminu Bello Masari ya kai ziyarar duba aikin ginin gidaje 185 da Gwamnatin ke ginawa a kusa da Asibitin kwararru (FMC) dake nan Katsina.

Gwamnan wanda Shugaban hukumar samar da gidaje ta jiha, Alhaji Salisu Abubakar Daura ya zagaya dashi, ya nuna gamsuwa a kan yadda aikin yake tafiya.

Tun farko Alhaji Salisu Daura ya shaida wa Gwamnan cewa rukunin gidajen ya kunshi gidaje 127 masu dakunan kwana ukku-ukku sai kuda 58 wanda suke da dakuna bibbiyu. Kuma a halin yanzu an kammala da dama saura kuma na kan hanya.

Ya bayyana cewa hukumar gyaran hanyoyi ta jiha (KASROMA) ita ke gudanar aikin hanyoyi mai tsawon sama da kilomita 5 wanda ya karade rukunin gidajen, sai kuma hukumar samar da wutar lantarki ta jiha (REB) da take aikin sanya wutar lantarki. Ita kuma hukumar samar da ruwa tana nan ta dukufa wajen ganin ta hada gidajen da ruwan famfo.

Gwamna Aminu Masari ya sami rakiyar Kwamishinan yada labarai na jiha Alhaji Yahaya Abdulkarim Sirika da kuma wasu manyan jami’an Gwamnatin.

GREENTIDE AGRO
GREENTIDE: Avert

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

MUN GANI A KASA A HUKUMAR KASROMA ~~~Cewar Alhaji Salisu Mamman CONTINENTAL

A ranar 18 ga watan Oktoba ne na shekarar 2021 wata Kungiya mai zaman kanta da ake kira "Mun Gani A Kasa" ta shirya...

Top 10 richest states in Nigeria;

Top 10 richest states in Nigeria; 1. Lagos - $33.68 billion Lagos tops the list of the top 10 richest states in Nigeria. It is also...

Tsohon Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi II da Sheikh Maƙari, Babban limamin Abuja Sun garzaya Senegal wajen bikin Mauludin Annabi S.A.W

Sarki Muhammadu Sanusi Lamido da Sheikh Makari sun shilla kasar Senegal domin halartar Maulid Annabi Muhammadu SAW. Rahotanni Cikin Hoto na Cewa Mai martaba sarkin...
%d bloggers like this: