GWAMNAN KATSINA DA DALIBAN FIRAMARE

daga Abdulhadi hadi bawa
Ss a social media

Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga iyaye da su rika jusriyar sa ido da kula da tarbiyyar ‘ya’yan su mata, madadin su rika hana su zurfafa Ilimin su zuwa matakan gaba da Sakandare.

Alhaji Aminu Bello Masari ya yi wannan kiran ne yau a fadar Gwamnatin Jihar Katsina yayin da ya karbi bakuncin daliban makarantun Firamaren Gwamnati da suka wakilci jihar Katsina a gasar karatu da rubutu ta kasa da kuma gasar muhawara da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Duk da cewa wadanda sukai gasar muhawara sun tsaya ne a matakin kusa da na karshe (quarter final), sun doke wakilan jihohi da dama har da na babban birnin tarayya Abuja.

A daya bangaren kuwa, wadda ta wakilci jihar Katsina a gasar karatu da rubutu kuwa, wadda dalibai ce a Makarantar Firamaren Gwaji ta Gwamnati (Model Primary) dake Faskari mai suna SUWAIBA HASSAN, ita ta lashe gasar, a inda tazo ta daya a jerin wadanda suka shiga gasar.

Wannan nasara da ta samu, tasa jihar Katsina tazo ta daya a wannan gasa da duka jihohin kasar nan suka shiga.

Gwamna Masari ya jinjina ma wadannan dalibai musamman Suwaiba Hassan saboda wannan kokari da sukayi. Ya kuma mika godiyar Gwamnatin jiha ga Malaman wadannan yara da kuma shuwagabannin hukumomin ilimi a matakan kananan hukumomi da jiha.

A nashi jawabin, Shugaban hukumar Ilimin bai daya ta jiha (SUBEB) Alhaji Lawal Buhari, ya bayyana cewa wannan nasarori da ake ta samu, sakamako ne irin namijin kokarin da Gwamnatin Jiha keyi a bangaren ilimi. Ya kuma yaba wa Gwamna Aminu Bello Masari saboda irin tsayuwar dakan da yayi wajen an gyara harkar ilimi, musamman a wannan mataki na Firamare.

A nashi bangaren, Mahaifin Suwaiba, Malam Hassan, godiya yayi cikin shauki, ga Gwamnatin Jiha, shuwagabannin hukumomin ilimi da kuma Malaman makarantun da suka zage damtse wajen ganin sun ba yaran kulawar da ta kamata wadda har ta kai su ga wannan mataki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here