Gwamna Aminu Bello Masari ya shiga birnin Kano yau domin yin ta’aziyya ga masu martaba Sarakunan Kano da Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero da Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda suka rasa Mahaifiyar a ranar Asabar 24 ga watan Afrilu da ya gabata.

Mahaifiyar tasu Hajia Maryam Ado Bayero Yaya ce ga Maimartaba Sarkin Ilori Alhaji Ibrahim Sulu Gambari kuma surukar Sarki Muhammadu Sanusi II (Murabus).

Daga fadar Sarkin, sai Gwamna Masari ya wuce gidan tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu wanda shi ma yayi rashin tashi Mahaifiyar, Hajiya Hafsat, a ranar Alhamis da ta gabata.

Gwamnan yayi addu’ar Allah Ya jikan su da Rahamar Shi kuma Ya albarkaci bayan su, Ya kuma basu hakuri.

Ya kuma roki Allah Ya jikan sauran Musulmi da suka rasu ta dalilai daban daban, musamman wadanda ake kashewa ba suji ba basu gani ba. Allah Ya gafarta masu Ya tallabi bayan su kuma Ya azurta mu da zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here