Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya halarci taron kaddamar da littafi mey taken “LIFE AND POLITICS OF ALIYU SABO BAKINZUWO 1934-1989” wato tarihin siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kano Alh. Aliyu Sabo Bakinzuwo wanda SS SHATSARI ya wallafa.

An kaddamar da littafin a dakin taro na Sani Abacha dake Kofar Mata, Gwamnonin jihohi da dama da manyan yan kasuwa da yan siyasa sun halarci bikin kuma sun sayi kwafin littafin. Gwamnatin jihar Kano da shugabancin kananan hukumomi suma sun sayi kaso mafi yawa na littafin akan kudi N7Million, wanda za’a tura littafan dakunan karatu domin dalibai su karanta kuma su amfana da koyi da irin rayuwar marigayin.

Daga karshe Gwamnan yayi addu’a da Allah ya jaddada Rahma gare shi Allah kuma Ya cigaba da kulawa da bayan sa Ya baiwa iyalan sa damar koyi da kyawawan halayen sa.

Gwamna Ganduje na tare da Mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da kuma Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da manyan jami’an gwamnatin jiha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here