Gwamnan Jihar Zamfara Ya tube Hakimi Saboda Zargin Saida Makamai ga Yan Fashin Daji

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle Ya dakatar da Hakimin Badarawa dake masarautar Shinkafi a Jihar Surajo Namakkah daga sakamakon bada sarauta wa wani jami’in soji da ake zargi da saida makamai wa yan fashin daji.

Gwamnan Ya ce Jihar ba za ta lamunci duk wani lamari da zai tarwatsa zaman lafiyar Jihar ta Zamfara ba.

A yau Juma’a ne dai gwamnan ya sanar da wannan dakatarwa ta bakin Daraktan Yada Labaran shi Yusuf Idris.Gwamnan ya kara da cewa duk wand gwamnati ta kama da kashi a duwawu, to lallai babu shakka sai ya ɗanɗana Kuɗar shi.

Matawalle ya kuma ce daga yanzu duk wani masarauci da zai karrama wani da wata sarauta to tilas sai ya nemi izini daga gwamnati don gudun abinda zai kai ya komo.

A cewar gwamnan, shi wannan jami’in soja da aka naɗa a baya bayan nan an chafke shi da zargin saida alburusai sama da ashirin wa yan fashin daji.

An chafke jami’in sojin ne yayin da yake gab da damka alburusan ga wani Mai suna Bashiru Maniya dake garin Shinkafi, wanda kuma da ma tuni har ya karbi Fashin alkalami na Naira dubu dari.

-Dimokuradiyya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here