Gwamnan Bayelsa ya jinjinawa kansilar da ta sarayar da motarta dan gina gada a kauyensu

Gwamnan jihar Bayelsa Sanata Duoye Diri ya yaba tare da jinjinawa Hon. Onem Tyna Miracle saboda yadda ta sarayar da kudin sayan mota da aka bata domin gina gada a kauyensu.

Kansilar wadda ke wakiltar mazaba ta biyu a karamar hukumar Ogbia, ta bayyana cewar ta kashe kudin sayen motar ne domin aikin da yake ciwa kauyen nasu tuwo a kwarya, tace lokacin da ta shaidawa dattawan yankin nasu cewar zata yi aikin da kudin da aka bata sunyi kokarin hanata, a cewarsu aikin yafi karfinta.

Haka nan, kansilar ta dage sai ta yi aikin wanda ya hada wasu kauyuka biyu da juna. Jin wannan labari, Gwamnan jihar Duoye Diri ya gayyaci Kansilar domin jinjina mata tare da yabawa wannan kokari da ta yi.

A sakamakon haka Gwamnan yace a Gwangwaje Kansilar da sabuwar fil irin wadda take so. Mutanan kauyen sun yabawa kokarin da Kansilar tasu tayi wajen wannan muhimmin aiki.

Daily Nigerian Hausa ta rubuta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here