Advert
Home Sashen Hausa Gwamna Tambuwal ya kafa sabbin dokoki a Sokoto

Gwamna Tambuwal ya kafa sabbin dokoki a Sokoto

Daga Yusuf Gidan Dare

Gwamna Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal na jahar Sokoto ya aminta da kafa dokoki domin ganin an magance matsalar tsaro a wasu yankunan jahar Sokoto dake fama da Yan Ta’adda Ga dokokin kamar haka;

1 An Haramta Bi hanyar Marnona Zuwa karamar Hukumar Isah har sai baba tagani daga yau. A Don haka ake ba matafiya da ababen hawa shawara da subi hanyar Goronyo-SabonBirni-Isah

2- an haramtawa Manyan motoci/ Sauran ababen hawa masu daukar itacen girki shiga dajin Daga yau.

3- An haramta siyarda kowacce irin dabba a kasuwannin kananan hukumomin Gada, Goronyo,Gudu, Illelah Isah Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal Tangaza, Tureta, da Wurno.

4-An haramta daukar Dabbobi da manyan motoci da sauran ababen hawa a kananan hukumomin Gada, Goronyo,Gudu, Illelah Isah Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal Tangaza, Tureta, da Wurno.

5- An haramta daukar mutum uku akan Babur daya da kuma fiyeda mutum 3 a mashin mai kafa 3 (Agwagwa).

6- An haramta siyarda tsoffin babura ko kuma wadanda aka taba amfani dasu a kananan hukumomin Gada, Goronyo,Gudu, Illelah Isah Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal Tangaza, Tureta, da Wurno

7- An haramta amfani da Babur da kuma Keke-Napep daga 10pm na dare zuwa karfe 6am na safe a cikin babban birnin jaha, haka ma an haramta hakan daga karfe 6pm na yamma zuwa 6am na safe a kananan hukumomin Gada, Goronyo,Gudu, Illelah Isah Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal Tangaza, Tureta, da Wurno.

8- An haramta siyarda Man petrol ga yan bunburutu (Black Markets) Ko kuma siyar musu a gidajen mai.

9- Gidajen mai kadai da aka aminta dasu zasu siyarda man Fetur da diesel Wanda bai wuce 5000 ba a kananan hukumomin Gada, Goronyo,Gudu, Illelah Isah Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal Tangaza, Tureta, da Wurno.

10- Maaikatan da kadai zasu iya amfani da babura da keke-napep a lokacin dokar sune MAAIKATAN LAFIYA, JAMI’AN TSARO, YAN JARIDA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: