Rahotanni sun nuna cewa gwamnan jihar Kaduna ya bukaci fadar shugaban kasa ta sanya baki a rikicin da ke tsakanin sa da kungiyar kwadago ta kasa NLC, abin da ke nuna cewa Nasiru El Rufa’i yaji tsoro saboda NLC ta fi karfin sa.

Daga cikin wadanda Nasiru El Rufa’i ya tattauna da wadanda ya bukaci su shiga tsakani sun hada da: Boss Mustapha SGF, shugaban ma’aikata da kungiyar gwamnonin Najeriya.

Nasiru El Rufa’i ya debo wa kansa tafasasshen ruwa, kuma kungiyar NLC ta Najeriya da yan Nigeria sunfi karfinsa, don haka ya ji tsoro, shiyasa ya bukaci a taimaka masa domin a shiga tattaunawa da kungiyar Kwadago ta Najeriya don sasantawa kan batun yajin aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here