
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i na ganawa da majalisar Sarakunan jihar a halin yanzu a ɗakin taron gidan gwamnati.

Sai dai ba a san dalilin zaman ba amma bai rasa nasaba da batun naɗin Sarkin Zazzau, duk da cewa akwai jita-jitar dake yawo cewa akwai yiwuwar Gwamnan zai ƙirƙiro da wasu sabbin masarautu biyu a ƙarƙashin masarautar Zaria.