MASARI YA KAI ZIYARAR JAJE A SOKOTO

daga shafin Abdulhadi bawa

Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga ‘yan kasuwar da ibtila’in gobara ya shafa a babbar kasuwar garin Sakkwato dasu ɗauki wannan lamari a matsayin ɗaya daga cikin irin jarabce jarabcen da Madaukakin Sarki Allah Yayi rantsuwar zai yi mana a cikin rayuwar mu.

Gwamna Aminu Masari yayi wannan kira ne yau a Sakkwaton yayin da ya kai ziyarar jajantawa ga al’umma da kuma Gwamnatin Jihar bisa gobarar da ta afku a ranar talatar satin da ya gabata a kasuwar da ake kira da Kasuwar Shehu Shagari wadda take a cikin birnin na Sakkwato.

Alhaji Aminu Bello Masari wanda takwaran shi na Sakkwato Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya tara, ya yi addu’ar Allah Ya maida masu mafi alkhairi tare kuma da kare afkuwar haka nan gaba.

Gwamna Aminu Bello Masari ya sami rakiyar Shugaban kamfanin jiragen sama na Max Air da kuma wasu muƙarraban shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here