Gwamna Masari ya kai ziyara a ma’aikatar ma’adanai da ƙarafa ta tarayya…

A ci gaba da kokarin da Gwamnatin Jiha take yi na ganin ta dogara da kanta ba tare da ta’allaka kan kudin dauni na tarayya ba, Gwamna Aminu Bello Masari ya kai ziyara Ma’aikatar kula da ma’adanai da karafa ta tarayya domin neman goyon baya da hadin guiwa domin cinma wannan manufa.

A yayin wannan ziyara, Alhaji Aminu Bello Masari ya shaida wa Ministan cewa, tun kafin aba kasar nan ‘yanci, lardin Katsina yake taka muhimmiyar rawa wajen samar da kudin shiga da akayi amfani dasu wajen gina yankin Arewa har da ma kasar Najeriya gaba daya. Duk kuwa da cewa a lokacin kusa Noma da Kiwo ne kadai manyan hanyoyin samun kudin.

Ya bayyana cewa a yanzu haka jihar tana dauke da dumbin ma’adanan da idan aka fito dasu aka ririta su hakika za su bunkasa arzikin jihar da na al’ummar ta. Yin hakan, zai janye akalar ci gaban jihar daga jiran kaso daga lalitar tarayya zuwa ‘yancin cin gashin kai.

Saboda haka, sai yayi kira ga Ma’aikatar da ta shigo cikin lamarin domin idan duk aka fahimci cewa kowace jiha tana da arzikin da za ta rike kanta, to duk wadancan kiraye kiraye da ake na a raba kasa da kuma na ayi federaliyya ta fuskar da wasu suka fahimta duk za su kau.

A nashi jawabin, Ministan kula da Ma’adanai da karafa na tarayya, Olamilekan Adegbite ya bayyana cewa alhakin kula da ma’adanai duka yana kan Gwamnatin tarayya ne, amma ana ba kowace jiha kaso sha ukku bisa dari (13%) na duk kudin da aka samu daga ma’adanan ta, kana kuma a raba sauran kashi tamanin da bakwai tare da ita da sauran jihohi. Da wannan ne ya kara yin kira ga jihohin kasar nan dasu rika la’akari da dokokin kasa wajen yin nasu dokokin da suka shafi ma’adanai da albarkatun kasa domin kauce ma samar da yanayin da zai hana masu zuba jari shigowa.

Kwamishinan Ririta Albarkatu na jiha Alhaji Abdullahi Imam ya bayyana cewa an shirya tare da kawo wannan ziyara ne domin haska ma duniya kokarin da Gwamnatin Jiha take kai na habaka bangaren ma’adanai domin ganin jihar ta tsaya da kafafuwanta.

Haka kuma, Gwamna Aminu Bello Masari ya kai irin wannan ziyara ga Ministan kula da Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari na tarayya Otumba Richard Adeniyi, a inda Gwamnan ya nemi goyon bayan ma’aikatar wajen tallata albarkatun da Jihar take dasu da kuma nemo wadanda za su zuba jari a bangaren hakowa da kuma sarrafa albarkatun.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here