Home Sashen Hausa GWAMNA MASARI YA HALARCI TARON KADDAMAR DA FAIFAN CD NA TARIHIN RAYUWAR...

GWAMNA MASARI YA HALARCI TARON KADDAMAR DA FAIFAN CD NA TARIHIN RAYUWAR MAULANA SHEIKH (DR.) DAHIRU USMAN BAUCHI

GWAMNA MASARI YA HALARCI TARON KADDAMAR DA FAIFAN CD NA TARIHIN RAYUWAR MAULANA SHEIKH (DR.) DAHIRU USMAN BAUCHI

Abubakar Shafi’i Media Crew

Dr Bashir Usman Ruwan godiya, mai bawa Gwamna masari shawara akan Ilimi mai zurfi

Ranar Asabar 14, November, 2020 Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masari CFR, (Dallatun Katsina) ya bayyana Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin Mashahurin Malami, kuma Uba wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga koyar da ilimin addinin Musulunci musamman AlQur’ani da Hadithi da Fiqhu domin kara daukaka addinin musulunci bisa doran duniya.

Gwamnan Wanda shi ne Babban Mai Masaukin baki a taron, wanda ya samu wakilcin Mai bashi shawara na musamman a harkar ilimi Mai zurfi, Muhammad Bashir Ruwan godiya, ya bayyana Maulana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin Wanda ya bayar da gagarumar gudunmuwa ta ilmantar da al’umma a cikin Nigeria da kasashen waje.

Wakilin Gwamnan Yace” shi da kansa (Gwamna) da Miliyoyin a’ummar Jihar Katsina suna cigaba da amfanuwa da irin tafsirai da wa’azozi da nasihohi da addu’o’i da shawarwari daga wannan bawan Allah Mai daraja Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Gwamna Masari sai ya yi kira ga al’umma da su yi kokarin daukar koyon darussa na gari daga ayyukan yada addini da hada kan jama’a wanda Maulana Sheikh Dahiru Bauchi yake gudanarwa a cikin Kasar na tamu mai albarka dama kasashen waje.

Dalilin haka ne Gwamna Masari yace” yaba da gudunmuwa ta naira Miliyan Biyar ta Gwamnatin jiha da kuma naira Miliyan Biyar tashi shi Alh Aminu Bello Masari domin nuna kauna da girmamawa da jin dadin ayyukan alkhairi da Shaihinmu Dahiru Bauchi yake yima al’ummar Musulmin Kasar nan dama na kasashen waje.

A lokacin da Sheikh Dahiru Usman Bauchi, OFR yake gabatar da Jawabinsa ya bayyana Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari CFR, wanda yake ba Addinin Musulunci gaggarumar gudummuwa, dalilin hakan yasa suka zabeshi a matsayin Babban bako na Musamman a wannan taro. Daga karshe Sheikh yayi Addu’o’i sosai ga jihar Katsina da Kasa baki daya Allah ya bamu zaman lafiya.

Daga cikin Wanda suka raka Mai Mai Baiwa gwamnan shawara wanda ya wakilci Gwamna, akwai Deputy Accountant General Alh Sani Lawal BK (Madawakin Majidadin Katsina), Alh Abdulkadir karfi Liaison Officer Abuja sai CEO Na mobile Media Crew Alh Abubakar Shafi’i Alolo.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

CUTAR KORONA, BABU WANI ILLA DA YA NUNA WA SHUGABA BUHARI BAYAN YIN RIGAKAFI KORONA.

CUTAR KORONA, BABU WANI ILLA DA YA NUNA WA SHUGABA BUHARI BAYAN YIN RIGAKAFI KORONA. Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren...

Bazamu sake yin yarje-jeniya da ‘yan bindiga ba saboda sunci amanar mu- Aminu Bello Masari

Ba Za Mu Kara Yin Sassanci Da ‘Yan Bindiga Ba A Katsina, Saboda Sun Ci Amanar Yarjejeniyar Sulhun Har Sau Biyu, Cewar Gwamna Masari Gwamnan...

Masari: Gumi Should Preach Implications of Killing People to Bandits not Amnesty

Masari: Gumi Should Preach Implications of Killing People to Bandits not Amnesty The Katsina State Governor, Aminu Bello Masari recently spoke to select journalists on...

Stop Demanding Amnesty for Bandits, Query Them for Killings, Masari Tells Gumi

Stop Demanding Amnesty for Bandits, Query Them for Killings, Masari Tells Gumi •Says majority of herders living in forest today are bandits Francis Sardauna in Katsina Governor...

Katsina Govt. to repatriate 7,893 Almajirai to states of origin

Katsina Govt. to repatriate 7,893 Almajirai to states of origin Katsina State government has approved the repatriation of 7,893 Almajirai from the state to their...
%d bloggers like this: