Gwamna Aminu Bello Masari yayi kira ga sabbin Shuwagabannin Jam’iyyar APC na jihar da susa tsoron Allah a cikin wannan nauyi da Allah Ya nufe su da dauka.

Gwamnan yayi wannan kiran ne a jawabin da ya gabatar a wurin rantsar da sabbin shuwagabannin wadda akayi bayan tabbatar dasu da wakillan ‘yan jam’iyyar daga kowane sako na jihar nan sukayi a taron jam’iyyar na jiha (State Congress) da ya gudana a filin wasa na Muhammadu Dikko dake nan cikin garin Katsina.

Alhaji Aminu Bello Masari ya kara da cewa, ta haka ne kadai za su sai ma kawunan su rigar mutunci daga wurin ‘ya’yan wannan jam’iyya mai albarka, hakan kuma zai taimaka wajen daga darajar jam’iyyar tare da samun nasarar ta a zabuka masu zuwa.

Gwamna Masari ya shaida wa mahalarta wannan taro cewa masu ruwa da tsaki na wannan jam’iyya suka yanke hukuncin amfani da tsarin sasanci cikin fahimta wajen zabar shuwagabannin jam’iyyar tun daga matakin yanki (ward), zuwa na karamar hukuma har ya zuwa na jiha, wanda wannan tsari yana cikin wadanda tsarin mulkin jam’iyyar ya aminta dasu.

A karshe ya kuma yi kira ga sauran ‘yan jam’iyyar ta APC da suci gaba da bada goyon baya da hadin kai ga shugabanci da kuma jam’iyyar kanta domin dorewar ci gaban jihar da kasa baki daya.

A yanzu, shugabancin jam’iyyar, wanda Kwamishinan Shari’a Barista Ahmed Usman El Marzuk ya rantsar, yana karkashin jagorancin tsohon Sakataren jam’iyyar Alhaji Sani Aliyu Muhammad wanda ya fito daga shiyyar Daura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here