Home Sashen Hausa Gwamna Aminu masari ya jajantawa Iyayen ɗalibai da ƴan taadda suka sace...

Gwamna Aminu masari ya jajantawa Iyayen ɗalibai da ƴan taadda suka sace a makarantar kimiyya da fasaha dake ƙanƙara

A cikin alhini da matukar jimami, Gwamna Aminu Bello Masari ya jajanta ma iyayen daliban da ’yan ta’adda suka ɗauka a makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati dake Kankara.

Gwamnan ya bayyana cewa duk da Gwamnatoci suna ci gaba da daukar duk matakan da suka kama wajen shawo kan matsalar tsaro da muke ta fama da ita a sassa daban daban na kasar nan, wannan hari ya kara tabbatar da muna cikin halin jarabawar da dole mu koma ga Allah domin samun dauki Ya kuma yaye mana.

Alhaji Aminu Bello Masari wanda ya gana da hukumar makarantar, iyayen dalibai da kuma iyayen kasa, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro suna kan bin sawun ‘yan ta’addar da zimmar ceto wadannan yara.

Domin kuma kauce wa yiwuwar samun irin wannan hari a nan gaba, Gwamnan ya bada umurnin a rufe duk illahirin makarantun kwana na Gwamnati dake fadin jihar nan.

Wadanda suka rufa wa Gwamnan baya su ne Mataimakin shi Alhaji Mannir Yakubu da wasu manyan jami’an Gwamnati.

Ya Allah mun kawo kukan mu gare Ka, Ya Allah Ka share mana hawayen mu.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: