Advert
Home Sashen Hausa GWAMNA AMINU BELLO MASARI YAKAI ZIYAR DUBA AIKI A GIDAN KATSINA DAKE...

GWAMNA AMINU BELLO MASARI YAKAI ZIYAR DUBA AIKI A GIDAN KATSINA DAKE BINNIN TARAYYA ABUJA .

GWAMNA AMINU BELLO MASARI YAKAI ZIYAR DUBA AIKI A GIDAN KATSINA DAKE BINNIN TARAYYA ABUJA .

Da safiyar yau ne maigirma Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon.Aminu Masari yaje ziyarar duba aiki a gidan Katsina da gwamnatinshi take gyarawa tare da daukaka darajar gidan dake central Area cikin birnin tarayya Abuja.

Kafin zuwan gwamnatin Dallatu Aminu Bello Masari gidan a yashe yake inda ya zama kango,amma cikin yarda Allah mai girma Gwamna Aminu Bello Masari yake gyara gidan tare da maidashi na zamani Wanda kuma idan an gama aikin gwamnatin jihar Katsina zata bada wajen haya ga yan Kasuwa domin samar ma jihar Katsina da kudin shiga.

Mai girma Gwamnan ya samu rakiyar wasu daga cikin jami’an Gwamnati da suka hada da Kwamishinan yada labarai Abdulkarim Yahya Sirika,Dr.Bashir Usman Ruwan godiya, mai ba mai girma Gwamna shawara akan ilimi mai zurfi,Alh Dayyabu Safana Mai ba Gwamana shawara akan sha’anin gwamnati tare da rakiyar mai duba aikin Injiniya Chike Nathaniel, haka zalika yayin duba aikin Injiniyan dake kula da aikin ya tabbatar ma mai girma Gwamna cewa insha Allah zuwa karshen watan Nubamba na wannan shekara zasu kammala aikin.

Mai girma Gwamnan ya yaba kwarai da ya gane ma idonshi yadda aikin ke tafiya,kuma ya nuna gamsuwarshi da yanayin aikin.


Bashir Ya’u
Special Assistant (S.A)
On new Media Katsina Zone.

Advertisement:GREENTIDE AGRO
Advertisement:GREENTIDE AGRO

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Yanda aikin samar da Ruwan Sha, yake gudana a cikin Birnin Katsina… Gwamna Amin Bello Masari ya zagaya

A ci gaba da aikin gyaran ruwan cikin birnin Katsina da kewaye, a yau, Gwamna Aminu Bello Masari ya zagaya wuraren da muhimman ayyukan...

MU NA GAB DA AIWATAR DA ZABUKAN KANANAN HUKUMOMI, ZAKUMA MU SAMAR DA YANAYIN DA MANOMA ZA SU YI NOMA CIKIN NATSUWA

Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa Gwamnatin Jiha, hadin guiwa da jami'an tsaro da kuma masu ruwa da tsaki kan harkar tsaron,...

HOTO: Gwarazan Kokowa na ƙasar Nijar

Gwarzaye abin alfaharin NIGER 🇳🇪 Kamar yadda Kwallon yayi fice a Brazil, Kamar yadda Criquet yayi fice a India, Kamar yadda NBA yayi fice a USA, Kamar yadda...

Rundunar Ƴansandan Jihar Katsina tayi Nasarar chafke Barayin Babura…..

Rundunar ta bayyana yadda tayi Nasarar chafke Barayin masu fasa Gidajen Mutane suna satar masu Babura, a ranar 6/6/2021, bisa ga Rahotannin sirri rundunar...

KOWA YA KARE KANSHI DAGA HARIN YAN BINDIGA….

KOWA YA KARE KANSHI DAGA HARIN YAN BINDIGA....inji gwamnan zamfara Daga Hussaini Ibrahim, Gusau @ katsina city news A cigaban da bukikuwan cika shekaru biyu da Gwamnatin...
%d bloggers like this: