Gwamna Aminu Bello Masari ya kaddamar da Shirin nan na taimakekeniya don samar da ingantacciyar lafiya ga mazauna Jihar Katsina.

Ranar Talata 27/04/2021 Maigirma Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari CFR, ya kaddamar da Shirin nan na Taimakekeniya don samar da ingantacciyar lafiya ga mazauna Jihar Katsina Karkashin Hukumar taimakekeniyar lafiya ta Jiha.

A nashi Jawabin Shugaban Hukumar Alh. Muhammad T. Safana ya bayyana yanda hukumar ta fara kafuwa yace” kafa wannan hukuma ya biyo bayan Shawara da Hukumar NHIS ta baiwa Gwamnatin jiha don kulawa da lafiyar mazauna Jihar Katsina, Gwamna Aminu Bello Masari ya sanya hannu a kan dokar ranar 27 ga watan Disamba 2018.

Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya na Jihar Katsina Hon. Engr. Yakubu Danja yace” an kafa Wannan hukumar ne don ta habaka, ta daidaita, ta kula, ta kuma tabbatar an tafiyar da Wannan tsarin na Taimakekeniya kamar yadda ya kamata.

Daga cikin tawagar da ta rufama Gwamnan baya akwai Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha Muh’d Inuwa, Babban jojin Jihar Katsina Justice Musa Danladi Abubakar, Shugaban Mai’aikata na Jihar Katsina Alh. Idris Usman Tunes, Kwamishinoni tare da masu ba Gwamna Shawara da sauransu.

Abubakar Shafi’i Alolo
Chairman & CEO
Mobile Media Crew
28/04/2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here