Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci.

Taron da aka gudanar ranar Asabar 23/10/2021, a Babban dakin taro na masabkin shugaban kasa dake fadar Gwamnatin Jihar Katsina, ya tattauna akan matsalolin tsaro da kasar nan take fama dasu, wanda Jihar Katsina tana cikin Jihohin dake fama da wannan matsala.

Da yake gabatar da jawabinsa yayin da yake bude taron na yini biyu” Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya bayyana matsalolin tsaron da ya addabi Jihar Katsina, ya kara da cewa” ya zama wajibi Gwamnatoci su dauki duk matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma. Inda ya bayyana cewa” a nata bangaren, Gwamnatin jihar Katsina ta dauki matakai da dama domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar.

Gwamnan ya ci gaba da cewa” A cikin matakan da Gwamnatinsa ta dauka, akwai gyaran dokar kananan hukumomi wanda ya samar da kafa kwamitoci guda uku domin inganta huddatayya tsaro a tsakanin al’umma. Wadannan kwamitoci sun hada da, matakin Mai unguwa, Magaji da kuma Hakimi, wanda dukkansu suke a karkashin kwamitin matakin karamar hukuma wanda dama akwai shi tun farko.

Haka zalika, Gwamnati ta dauki wasu manyan matakai, ba don takura ma al’umma ba, sai don ganin an samu ingantancen tsaro a Jihar, matakan sun hada da, dakatar da hanyoyin sadarwa, takaita sayar da man Fetur da kuma takaita zirga zirgar babura da kurkura a fadin jihar.

Daga karshe Gwamnan ya jinjina ma Majalisar Dokoki ta jiha da kuma bangaren shari’a saboda irin goyon bayan da suke ba gwamnati wanda hakan ya samar da nasarori da dama wajen tafiyar da mulki da kuma jagorancin al’ummar wannan jiha musamman wajen aiwatar da dokoki.

Gwamna Aminu Masari ya” yaba ma kungiyar Kakakin majalisun Dokoki ta Jihohin da suka yi tunanin daukar matsalar tsaro a matsayin babban abinda da za su tattauna akan shi a wurin wannan taro, da kuma yadda suka zabi jihar Katsina, matsayin wurin da zasu gudanar da wannan taro mai matukar mahimmanci.

Tunda farko da yake gabatar da jawabin Maraba Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina Rt. Hon. Tasi’u Musa Maigari Zango, ya fara da godiya ga Allah (SWT) da ya ba Kungiyar shugabannin majalisun Dokokin Jihohi damar gudanar da wannan taro mai matukar mahimmanci, a Jihar Katsina domin neman makomar da ta dace ga ƙasa nan akan matsalolin tsaro da take fama dasu, ta hanyar taka mihimmiyar rawar da za ta kawar da rashin tsaro, rarrabuwar kawuna, rashin zaman lafiya da tattalin arziki.

Ya cigaba da cewa” wannan taron da ake gudanarwa a jihar katsina yana da matukar mahimmanci duba da jihar katsina tana ɗaya daga cikin jahohin da rashin tsaro ya yi ma katutu. Saboda haka a madadin Al’ummar jihar Katsina, ina farin cikin maraba da bakin mu, mahalarta wannan taro mai tarihi.

Kakakin Majalisar ya kara da cewa” dangane da dangantaka tsakaninmu, da Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, CFR, FNIM wanda ya nuna sha’awarsa akan wannan taron, ya taka mihimmiyar rawa wajen gudanar dashi, inda ya zama matsayin Babban Bako na Musamman, kuma wanda ya gabatar da Jawabi tare kuma da bude taron, yana da kyau mu nuna ma bakinmu muna matukar jin daɗin jagoranci na Mai Girma Gwamna.

Haka zalika ya kara da cewa” alaka tsakanin majalisar Zartarwa da majalisar Dokokin jihar Katsina tana tafiya da haɗin kai da mutunta juna. Ba abin mamaki bane haka, muna da haɗin kai mai ƙarfi wanda ya haifar da amincewa da Dokokin da muke zartarwa da ƙudurin da Membobinmu suke gabatarwa na ayyukan mazabu, wanda Gwamnatin take yadda da kuma aiwatar da su. Haƙiƙa muna matuƙar godiya da goyon baya da ake nuna mana.

Da yake gabatar da jawabinsa shugaban Kungiyar Kakakin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya Mai girma Rt. Hon. Abubakar Y. Suleiman ya bayyana cewa” Kungiyar Kakakin Majalisun Dokoki na jihohi (36) na Najeriya, an kafa ta ne don samar da wani dandalin tattaunawa da Kakakin Majalisun Dokokin, domin tattaunawa da bayar da shawarwari domin samar da mafita akan batutuwa da matsalolin da ke shafar membobin Kungiyar da ma kasa baki ɗaya.

Ya cigaba da cewa” Duba da rashin tsaro a kasarmu, yau ya dauki wani yanayi mai tayar da hankali don haka ya zama babbar barazana ga ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya da hadin kan al’ummar kasa. Wannan yasa muka shirya wannan taro, ya zama dole mu hada hannayenmu wuri daya don yaƙar barazanar rashin tsaron da muke fama da ita don cigaban ƙasarmu.

Ya kara da cewa” A matsayinmu na wakilan Al’umma daga sassan ƙasar nan, hakika mun damu kwarai da gaske akan mummunan yanayin barazanar rashin tsaro da ya addabi ƙasar nan. Don haka mun kira” wannan taro ne domin tattaunawa da bayar da shawarwarin da zasu samar da mafita akan wannan matsala, a cikin aikinmu da tsarin mulkin kasar nan ya ba mu dama.

Daga karshe ya” yaba ma Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, akan yadda yake kokari da jajircewa domin ganin ya kawar da masu aikata ayyukan ta’addanci a jihar Katsina. Ya kara da cewa” suna da tabbacin nasarorin da ake samu a yaƙi da rashin tsaro da gwamnatin jihar Katsina a ƙarƙashin Jagorancin Mai girma Gwamnan, basu samu ba, sai tare da goyon baya da haɗin kan Majalisar Dokokin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Rt Hon Tasi’u Musa Maigari Zango.

Don haka, muna yaba ma shugaban majalisar Dokoki ta Jihar Katsina da ma sauran abokan aikinsa a majalisar bisa goyon baya da hadin kai da suke bayarwa wajen yaki da rashin tsaro. Ya kuma roki ‘yan majalisar da su ci gaba da ba da goyan baya ga Mai girma Gwamnan domin ci gaban Al’ummar jihar Katsina.

Shugaban kungiyar shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya Hon. Abubakar Y. Suleiman ya mika sakon godiya ta musamman ga Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, A madadin Shugabannin Majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) da ma daukacin ‘Yan Majalisun Dokokin Jiha 991 na Najeriya, a kan yadda ya karbi bakuncin wannan muhimmin taro.

Daga karshen taron mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina Hon. Shehu Dalhatu Tafoki ya gabatar da jawabin godiya Amadadin Membobin majalisar Dokoki ta Jihar Katsina. Taron ya samu halartar Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari, mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Qs. Mannir Yakubu, yan majalisar zartarwa da majalisar Dokoki ta Jihar Katsina. Dadai sauransu.

Rahoto
Surajo Yandaki

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here