A ranar Talata 12/10/2021, akai bikin rantsuwar a dakin taro na fadar Gwamnatin Jihar dake katsina.

Daga cikin wadanda gwamnan ya rantsar sun hada da, Justice Ibrahim Isyaku Mashi, Justice Kabir Sha’aibu da Justice Abubakar Ibrahim Maude. Da yake tsokaci Jim kadan bayan da ya rantsar da Mayan Alkalan, Gwamna Aminu Bello Masari ya fara da Godiya ga Allah (S.WT.) Wanda da ikonsa ne wannan bikin rantsuwa ya tabbata.

Ya kara da cewa” Gwamnatin Jihar katsina tana bakin kokarinta, wajen ci gaba da tsarin sauya kotuna da tsarin shari’a zuwa matakin da zai kara ciyar dasu gaba. Haka zalika gwamnatin Jihar katsina, za ta ci gaba da tallafa ma bangaren shari’a don yin kyakkyawan aiki tare da tafiya kafada da kafada da shi. Daga karshe Gwamnan yaja hankalin wadanda aka rantsar da suji tsoron Allah su rike aikinsu da mahimmanci don ciyar da bangaren shari’a gaba, a Jihar Katsina.

Bikin rantsuwar ya samu halartar Mataimakin gwamna jihar katsina Qs Mannie Yakuba, Sakataren Gwamnatin Jihar katsina Dr. Mustapha muhd inuwa, Kwamishinan shari’a kuma Babban Lauya na Gwamnatin Jihar Katsina Barr. Ahmed Usman El-murzuq, Babban Jojin jahar katsina Mai Shari’a Musa Danladi. Girandi khadi na Jihar katsina.

Sauran sun hada kakakin majalisar Dokokin jihar katsina, Wanda ya samu wakilcin shugaban masu rinjaye na majalisar Hon. Abubakar Suleiman Abukur, Dan majalisa Mai wakiltar karamar hukumar katsina Hon Aliyu Abubakar Albaba Yan uwa da abokan arziki. Da dai sauransu.

Abdulrashid Musa
Director Photography/Reporter
Mobile Media Crew
October 12/2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here