Gwamna Aminu Bello Masari da Gwamnonin Arewa, basu Shaƙare Jam’iya APC ba… -Mansir Ali Mashi-

Gwamnonin Arewa 3 da tawagar Sarakunan Arewa da sukaje Ziyarar Jaje a Gwambe kwanakin baya

A wani tattauna da Katsina City News tayi da Dan majalisa mai wakiltar Mashi da Dutsi a Majalisar tarayya Hon. Mansir Ali Mashi, ya bayyana takaicin sa dangane da wasu da suke zargin Gwamnonin APC da cutar da Jam’iyyar.

Inda ya bayyana irin gudummawar da ko wane Gwamnan APC ke badawa a jihohin sa, yace “amatsayinsa na Danmajalisar tarayya, yana zirga-zirga daga Abuja zuwa wasu jihohin, kuma yana ganin irin tasirin ayyukan da ko wannen su, yakema Al’umarsa, don haka Gwamnonin APC sun bawa Jam’iyyar su gagarumar gudummawa a kowane matakai”.

Da ya waiwayo akan jihar sa ta Katsina, kuma Hon. Mansir Ali Mashi, ya yaba kokarin Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello masari, inda ya bayyana irin jajircewar sa domin ganin anyi zaben shuwagabannin jam’iyya tun daga matakin Ward zuwa kananan hukumomi, da na jiha a cikin Adalci da Kwanciyar hankali, inda yace, ba’a taba samun wani gwamna da yayi irin tsari da kokarin Aminu Masari ba. Ya bada misali da wasu Jihoyi musamman na yankin Arewa maso yamma, inda yace, sun samu bangarori daban-daban. Wannan ba karamin kokari bane, Muna godiya ga mai girma Gwamna, injishi.

Da Katsina City News tayi masa tambaya akan wasu masu ganin cewa, anyi rashin daidai, a shirya zaɓen, Mansir Ali Mashi, yace, idan ma akwai wani da yake zargin haka “nidai banji ba” to yana fadin son ransa, ne, saboda duk wanda ke cikin Jam’iyyar na haƙiƙa yasan Gwamna ya kamanta adalci, ya shirya kwamiti na Dattawa, da suka tsaya tsayin daka, don ganin komi ya tafi cikin tsari, kuma mai girma Gwamna baiyi masu katsalandan a cikin ayyukan su ba, don haka idan wani yazo yana ta surutu, to wannan bamu ma san ya yake so ayi ba.”

Da ya waiwayo akan ayyukan raya ƙasa da Ilimi, Hon. Mashi, yace kowa yasanni ada nine mai bawa Gwamnan katsina shawara’akan Rediyo da wayar da kan jama’a, yace mun zaga da ku, (‘yanjarida) duka kananan hukumomi guda 34 na jihar Katsina, kun gani da idon ku irin ayyukan da Maigirma Gwamna yayi, tsakanin tituna makarantu, da ruwan sha, kowa kam yasan yanda muka gaji Gwamnatin da ta shude, don haka muna godiya muna kara godiya, kuma mun yaba ma Maigirma Gwamna akan irin wannan namijin kokari, da yayi.

Da yake tsokaci game da sha’anin tsaro Hon. Mashi, yace Lallai kam wannan matsala tana damun mu tana damun Maigirma Dallatu Aminu Bello Masari, matsala ce da tashafi kusan jihohin mu na Arewaci, da yammacin kasar ga duk mai bibiyar kafafen yaɗa Labarai na waje yaji lokacin da na fito nace lallai abinci bangaren tsaronnan bayan matsalar da ta faru a ƙaramar Hukumar Batsari, don haka muna iyakacin kokari ta janibin mu, Muna fata Allah ya kawo karshen wannan jarabawa. Inji Hon. Mansir Ali Mashi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here