Advert
Home Sashen Hausa Gwamantin Jihar Kaduna Ta Rushe Kasuwar Samarun Zariya A Daren Jiya.

Gwamantin Jihar Kaduna Ta Rushe Kasuwar Samarun Zariya A Daren Jiya.

Masu kasuwanci a Samarun Zariya sun wayi gari sunga Gwammanatin jihar Kaduna tasa an rushe musu Shagunan su cikin dare.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

A safiyar yau Asabar ne 21 ga watan agusta 2021, masu kasuwanci a bakin titin samarun Zariya, suka tashi da ganinin wannan lamari na rushe musu shagunan da suke sana’a ba tare da sun kwashe komai na ciki ba, shi dai wannan rusau din an fara ne tun daga leader research dake daura da babban gate na jami’ar Ahmadu BELLO University Zariya, inda ya nufi north gate har zuwa kasuwan samaru , inda duk wata kwantena dake wajen aka rusa ta ko kuma aka lalatata.

Wannan yasa wadanda abin ya shafa suka tsunduma cikin alhini da tashin hankali , inda wasu ke kuka da takaici.

An tabbatar da cewa ma’aikatan dake kula da gine gine na jihar Kaduna KASUPDA hade da rakiyar jami’an tsaro ne sukayi rusau din cikin daren jiya Juma’a 20 ga watan agusta.

Masu karatu ko ya kuke kallon wannan rusau din da gwamnati take yi?

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Alleged Defamation: Gov. Masari demands N10bn, apology from journalists

Gov. Aminu Masari of Katsina State has demanded the payment of N10 billion as damages from Mr. Emmanuel Ogbeche and Mr. Ochaika Ugwu, Chairman...

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina…..

Biliyan Ɗari shida da Miliyan ɗari biyu da Hamsin, Tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin ɓunƙasa Karkara da gandun Daji a jihar Katsina..... A ranar Alhamis...

DIRECTOR-GENERAL INAUGURATES NYSC MEGA PRINTING PRESS

NYSC Director-General, Major General Shuaibu lbrahim today inaugurated the NYSC Mega Printing Press in Kaduna. He said the project, which was conceived almost a decade...

Shugaba Buhari Ya Miƙa Ta’aziyyarsa Ga Iyayen Hanifa, Yarinyar Da Aka Kashe A Kano.

Daga Zaharaddeen Gandu Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa 'yan sandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai...