Advert
Home Sashen Hausa GUMI: Yan Bindiga Sun Sanar Min Salon da Suke Bi Wurin Gujewa...

GUMI: Yan Bindiga Sun Sanar Min Salon da Suke Bi Wurin Gujewa Luguden Sojin Sama~Inji Sheikh Gumi

GUMI: Yan Bindiga Sun Sanar Min Salon da Suke Bi Wurin Gujewa Luguden Sojin Sama~Inji Sheikh Gumi

Sanannen malamin addinin Islama mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi ya kara tabbatar wa da jama’a cewa a koda yaushe yana kara samun damar tattaunawa da yan fashin dajin da suka addibi arewacin Najeriya.

A takardar da malamin ya fitar a kwanakin nan, ya bayyana cewa gungun yan bindigar sun sanar dashi cewa luguden ruwan wutan da sojin sama ke yi ba ya taba su, sai dai ya taba matansu da ‘ya’yansu domin kuwa suna da salon kauce musu kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gumi ya ce, yan bindigar sun kware tareda zama yan hannu wurin kauce wa duk duk wani Bam da sojin sama za su wurgo, hakan ne yasa dakyar a iya kama su ko halaka su.

“Abin da ba dole ku sani ba shi ne, yan bindigan sun kirkiro hanyoyin tserewa luguden wuta ta sama. Sun sanar damu cewa za ku iya kashe matansu da ‘ya’yansu ne kawai ta wannan harin”

“Abin nufi shi ne, idan aka matsanta musu a Zamfara, babu shakka zasu sauya wuraren zama. Toh dukkan Najeriya ce za ta kasance a wannan halin”?

“A zancen gaskiya, shari’a ce ke kare hakkokin jama’a . kudi da lokaci da aka yi amfani da su dakyau babu shakka zasu kashe cutar kuma zai gyara kasar nan, ya cire mata cutar ta’addanci da gurbatattun shugabanni”~Inji Sheikh Ahmad Gumi

Jaridar Sokoto

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: