BABBAR KOTUN TARAYYA DAKE KANO TA TSAIDA GOBE LITININ 28/6/2021 DON SAKE GURFANAR DA MAHADI SHEHU A CI GABA DA TUHUMAR SA DA LAIFIN BAZA TAKARDUN BOGI DA YUNKUNRIN TUNZURA JAMA’A TA HANYAR AMFANI DA YANAR GIZO.
–‐—————-‐———————–

Malam Mahadi Shehu a zaman Kotun da ya gabata a Kano

Idan za a iya tunawa an gurfanar da Mahadi Shehu a gaban Kotun tun a ranar wata Alhamis, 18/3/2021 inda ya musunta zargin da ake yi masa.

Akan haka aka dage shari’ar zuwa 19/4/2921 don soma sauraren shedu kana Alkali ya bada shi beli bisa sharadin a wuce da shi gidan yari har sai ya cika sharuddan belin.

Kafin zuwan ranar ne sai ma’aikatan Kotunan kasar nan gaba daya suka tsunduma cikin wani yajin aikin da ya kwashe sama da watanni biyu ana yi, wanda ya kawo tsaiko ga shari’ar.

Sai dai kuma a ranar Jumu’ar da aka sako Mahadi daga gidan yari na Kurmawa an ga wani faifan bidiyo na yawo wanda ya yanke hamzarin duk wani mai shakku game da lafiya ko rashin lafiyar Mahadi.

A halin da ake ciki kuma, ita ma Babbar Kotun sauraren daukaka kararraki ta Katsina ta tsaida gobe Litinin 28/6/2021 don bada bahasi akan koken da Mahadi Shehu ya shigar yana kalubalantar ingancin hanyar da Babbar Kotun Musulunci dake Katsina ta bi wajen sada shi da sammacin karar da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa ya kai shi akan zargin ya bata masa suna.

Za a saurari bahasin Alkalan uku da suka karbi koken a zaman su na Dutsinma karkashin jagorancin Maishari’a Musa Danladi Abubakar da karfe 9:00am a zauren Kotu ta 3 dake harabar kotu ta Jihar Katsina dake kan hanyar Daura.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne, da wane irin ilimbon ne zai zo Kotu gobe. Shin zai kara dawowa daure da janjami da makarin wuya da sandunan guragu ko kuwa zai yi irin na Senata Dino Melaye wanda aka kawo kotu a cikin motar daukar marasa lafiya (Ambulance).

A yi dai mu gani….
Daga shafin Abdullahi Aliyu yar adua jami in hudda da jama a na sakataren gwamnatin katsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here