Kwamitin da Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa karkashin jagorancin Alhaji Lawal Aliyu Daura, domin fitar da tsarin yadda za a aiwatar da shawarwarin da kwamitin bincike kan gobarar da akayi a babbar kasuwar Fatima Baika dake nan cikin garin Katsina ya bayar, ya mika rahoton shi a gaban taron Majalisar zartaswa ta jiha a yau.

Rahoton ya tabbatar da yawan asarar da akayi ta kayayyakin kusan Naira Biliyan Daya, ya kuma bayyana cewa ya zuwa yau, an sami gudummuwar kudi sama da Naira Miliyan Dari da Hamsin (N150m).

Wannan na cikin bayanin bayan taron Majalisar zartaswas da ya gudana yau a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari wanda Kwamishinan Shari’a Barista Ahmed Usman El Marzuk yayi wa manema labarai.

Ya kuma kara da cewa, bayan tattaunawar da Gwamnati tayi da shuwagabannin kungiyar kwadago ta jiha da sauran masu ruwa da tsaki, Majalisar zartaswas ta amince da a cire kashi ashirin cikin dari (20%) na albashin wata daya na Gwamna Aminu Bello Masari, Mataimakin shi Alhaji Mannir Yakubu da sauran duk masu rike da mukaman siyasa dake wannan jiha. Haka kuma sauran Ma’aikata wadanda suke a kan matakin albashi na 1 zuwa na 14 za a cire masu kashi ukku cikin dari (3%) na albashin su domin a hada a tallafa ma ‘yan kasuwar da suka tafka asara.

Wadanda suke matakin albashi na 15 zuwa 17 kuwa, ma’aikatar kudi ta jiha za ta lissafa kuma ta fitar da abinda ya kamata su bayar a matsayin nasu tallafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here