Rahotanni daga jihar Neja a Najeriya na cewa wasu yara biyu sun mutu sakamakon gobarar da ta tashi a gidansu da ke Anguwar Dawaki a garin Suleja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yaran – mace da namiji – wadanda da ke suna Suraiya da Habib, ba su wuce shekara tara a duniya ba.

Rahotanni sun ce mahaifin yaran, Alhassan Jibirin Yanji, ya samu raunuka a lokacin da ya yi yunkurin kubutar da yaran kuma yanzu haka yana kwance a wani asibiti da ke Suleja.

Hukumomi a karamar hukumar ta Suleja sun tabbatar da tashin gobarar suna masu cewa an kaddamar da bincike domin gano musabbabinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here