Gwamna Aminu Bello Masari ya yi kira ga mahukuntan Majalisar Dokoki ta jiha da hukumar kashe gobara ta jiha da suyi kokarin gano musabbabin gobarar da ta ƙone wani bangare na Majalisar da hantsin yau.

Gwamnan yayi wannan kiran ne bayan da ya duba zauren Majalisar wanda wani bangaren shi ne wutar ta shafa.

Alhaji Aminu Bello Masari ya kara jan hankali ga al’umma da a rika sa ido sosai tare da kula domin kauce ma irin wadannan ibtila’o’i.

Danmajalisa mai wakiltar karamar hukumar Kankia, Honorabul Salisu Rimaye ne ya zagaya da Gwamnan ya kuma nuna mashi irin ta’adin da gobarar tayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here