GINA TASHOSHIN LANTARKI A JIHOHIN BAUCHI DA NEJA

#GaskiyarLamarinNijeriya @Ko kunsani NG

Ko kun san cewa, Gwamnatin Shugaba Buhari ta kammala tare da ƙaddamar da sababbin ƙananan tashoshin lantarki a Darazo da ke Jihar Bauchi da Agaye da ke Jihar Neja?

Tashar Darazo ta na ƙunshe da ƙarfin 1X7.5MVA 33/11KV da 0.15km na layin 33kv da kuma 3km na layin 11KV tare da gina layin LT mai ƙarfin 8km. Hakan nan kuma ga samarwa tare da sanya layin LT, baya ga turansifomomi guda huɗu masu ƙarfin 300KVA.

A garin Agaye kuwa Gwamnatin Tarayya ta gina ƙaramar tashar lantarki mai ƙarfin layi 1X7.5MVA 33/11kv.

Wannan na daga cikin irin namijin ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Buhari ke yi wajen ganin ta inganta rayuwar al’umma ta fuskar walwala da farfaɗo da masana’antun ƙasar, don samar da aikin yi!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here