GIDAUNUYAR CONTINENTAL~~~ Tarihi ya Maimaita Kansa

GIDAUNUYAR CONTINENTAL~~~ Tarihi ya Maimaita Kansa

Daga Abdurrahman Aliyu.

A ranar latinin 19-4-2021.
Al’ummar karamar hukumar Rimi suka sheda tarin ayyukan alheri da Gidauniyar Continental take gudanarwa a karkashin jagorancin hazikin Dankasuwa, kuma bangon talakawa Alhaji Salisu Mamman Continental.

Idan ba a manta ba a shekarar da ta gabata ma wannan gidauniya ta raba kayan tallafi na miliyoyin nerori ga al’ummar karamar hukumar Rimi.

A wannan shekarar ma gidauniyar ta sake yunkurowa inda ta raba kayan azumi da kudade domin samar da sauki ga al’umma. An raba kayan ne zuwa mazabu goma na karamar hukumar.

A jawabinsa shugaban Gidauniyar ya bayyana cewa, “shi wannan tallafi da yake bada wa yana bada shi saboda lokacin da suke yara sun ga yadda kakanninsu suke rige-rigen taimakon junansu.

Haka kuma, ya yi bayani kan ginin da yake yi a babbar asibitin jiha mai cin gado 24 yace yanzu ya fadadashi zuwa gado 30 ginin zai ci naira miliyan 70.
Akwa Kuma ginin babban dakin taro mai cin dalibi 350 zuwa 400. Wanda shima zaici naira miliyan 60.

Ya yi kira ga sauran al’umma da a hada da hannu domin a taimaki al’umma, domin hannu daya baya daukar jinga, mai taro mai sisi daidai gwargwadon iko.

Kazalika ya kara da cewa nan da wani Dan lokaci mazabu da ke karamar hukumar Rimi zasu amfana da talafin Naira Miliyam 11 insha Allah.

A jawabin mai girma Sakataren gwamnatin Jihar Katsina Dr. mustapha Inwa ya nuna jin dadinsa kan wannan abun alheri, sanan ya yaba wa shugaban gidauniyar Continental Alh Salisu akan irin kokarin da yake wajan tallafawa al’umma, ya kara da cewa gwamnatin jihar Katsina tana Alfahari da irinsu Alh. Salisu wajan tallafa wa al’umma da samar wa matasa aikin yi kalkashin kamfaninshi na Continental computers.

Kayyakin daka raba sun hada da Buhunan masara 112 da buhun Gero, buhunna shinkafa 42, katin din taliya 152, sikari buhu 10, sai wake buhu goma. Sai kudaden jigilar kayan da kudin safgar dahuwar abinci naira 650,000.

Bayan nan an bayar da talllafin kudi ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC Naira 1,250,000 sai shugabanin jam’iyya a matakin mazabu da karamar hukuma naira 1,100,000. Sai wakilin rumfa ‘yan tara-tara naira 500,000. APC 2021 revalidation naira 3,000,000. Sai jam’iyyar APC shiyyar Katsina naira 200,000. An raba wa Limamai na masallantan juma’a izala da darika naira 600,000. Sai Rimi LG social media naira 50,000. Katsina social media naira 50,000. Suma kafafen yada labarai an Basu naira 50,000.

Baki daya an kashe jimillar kudi sama da Naira miliya 13.

Mutanen da suka hakarci taron sun hada da shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Shitu S Shitu da mataimakan sa na duka shiyoyi uku. Sauran sun hada da Hon. Nasiru Ala Iyatawa da Hon. Mu’azu Lemamu Tsagero da Hon. Bilyaminu Muhammad Rimi da Hon. Gambo Abdulkadir da wakilan Kauran Katsina da Majidadin Katsina tare da ‘yan siyasa na ciki da wajen karamar hukumar Rimi.
Aliyu dalibi ne mai karatun digri na uku a jami ar UMYU katsina. Kuma daya dag cikin editocin jaridar taskar labarai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here