Advert
Home Sashen Hausa GIDAUNIYAR CONTINENTAL TA RABA KAYAN MAKARANTA KYAUTA A RIMI

GIDAUNIYAR CONTINENTAL TA RABA KAYAN MAKARANTA KYAUTA A RIMI

Shugaban gidaunuyar continental Alh Salisu Mamman Kaɗanɗani ya kaddamar da tallafin kuɗi na naira miliyan ɗaya da kayan makaranta guda ɗari ukku da Arba’in (340) wanda yayi Alƙawarin ɗinka wa ɗalibai ɗari ukku da Arba’in (340).

Wadanda sukayi na ɗaya zuwa na goma wanda da yayi alƙawari sati huɗu da ya gabata ranar juma’a 27-8-2021 lokacin daya halarci taron bada hutun zango na biyu a makarantar firamare ta tunawa da Kaura Abdulkadir dake Rimi.

Yau Ranar juma’a 8-10-2021 ya jaddada Alƙawarin daya ɗauka na cewa zai ɗinka wa ɗalibai kayan makaranta guda 340 tare da tallafin kuɗi Naira miliyan daya.

Ya ɗinka uniform ɗin kuma ya bada su ga mai girma kauran Katsina hakimin Rimi Alh Nuhu Abdulkadir Rimi zuwa ga ɗaliban sannan daga cikin kuɗin yayi Alƙawari zai bada Naira miliyan daya ya fara bada chak na Naira dubu ɗari biyar 500K ga sakataren Ilimi na Rimi Alh. Salisu Ibrahim domin su fara aikin, zuwa wata na gaba zai ida cika sauran kuɗin Naira dubu ɗari biyar 500K su wannan kuɗi daya b ada, ya bada sune domin a a gyara wasu ƙananun matsalolin irin su gyaran ƙofa da taga kwanon da ruwa ya ɓanɓare da kuma bangayen da suka faɗi ƙasa kafin akawo wa makaranta ɗauki daga gwamnatin jihar Katsina

wannan agaji da gwamnatin jihar Katsina zata kawo ƙarƙashin jagorancin Rt Hon Aminu Bello Masari yana daga cikin ƙoƙarin Alh. Salisu Mamman yayi lokacin da yazo wajan bada hutu, inda ya gane wa idon shi halin da makarantar take ciki na rashin kujerun zama.

Awurin taron da yayi yau Alh Salisu ya tabbatar da cewa Insha Allah mai girma gwamnan zai zo firamare domin a sama azuzuwan da muke dasu guda 34 kujerun zama a makarantar tunawa da Kaura Abdulkadir dake Rimi.

Ya ƙara bayyana cewa mai girma gwamna kullin a shirye yake domin ya ga an taimaki harkar ilmi, Sannan ya ƙara da cewa gwamnan zai zo ya zaga ya Rimi domin yaga aikin titin (Township Road) da ke gudana yanzu da kuma aikin magudanar ruwa unguwar maliya dake cikin garin Rimi.

A wajan taron da aka yi yau Alh Salisu ya ƙara kira zuwa ga sarakunan gargajiya da ‘yan siyasa da masu kuɗi da ma’aikatan gwamnati da su haɗa kai a taimaki harkar ilmi dan baza mu sama gwamnati ido ita kaɗai ba sai abinda tayi mamu, mai taro mai sisi kowa yana iya bada daidai gwargwado ikon da mutum yake da shi amman ba hujja bace kome sai gwamnati tayi mamu.

Taron bayar da kayan ya samu halartar Kauran Katsina Hakimin Rimi, Alhaji Nuhu Abdulkadir da shugaban hukumar kula da gyaran hanyoyi ta jihar Katsina, Injiniya dakta Surajo Yazid Abukur da danmajalissa mai wakiltar karamar hukumar Rimi. Hon. Abubakar Suleiman Korau da sauran masu ruwa da tsaki da dama daga karamar hukumar Rimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: