GIDAN REDIYON COMPANION FM KATSINA: Sun Ziyarci Shaikh Yakub Yahya Katsina.

_Bin Yaqoub Katsina.

Gidan Rediyon na Companion FM sun ziyarci Shaihin Malamin ne a jiya Litinin da rana. Maƙasudin ziyarar dai shi ne; dan neman shawarwarin Shaikh Yakub da kuma neman addu’arsa kamar yadda sabon shugaban gidan rediyon na yanzu Mukhtar Abubakar Dutsamma ya ambata a jawabinsa na maƙasudin zuwansu. Haka kuma Wannan ziyara ta zo ne sakamakon ziyarorin da Sabon shugaban gidan rediyon ke yi ga iyayen al’umma a garin, kamar sarakuna da Malamai.

Shaikh Yakubu Yahaya Katsina ya basu shawarwari Musamman fadar gaskiya da kuma kiyaye haƙoƙin al’umma, yace wannan aiki nasu yana da lada da kuma albarka saboda aikin taimakon al’umma ne, sai dai yana da hatsari musamman idan ba a kiyaye kalmomin da za a yi amfani da su ba, inda magana ɗaya tal na iya jawo hautsinewar al’amurra. Haka kuma ya jinjina masu bisa ga ayyukansu musamman yadda suka keto ruwan sama suka zo, wannan ya nuna suna jajircewa a aiki, in ji shi.

Ya yi kira a garesu da su baiwa kowwa haƙƙinsa banda ɗaukar ɓangaranci na addini da mazhabobi. Ku sani kuna aikin al’umma ne, kuma ana buƙatar adalci ga kowwa, ya ankarar dasu.

Daga karshe yayi masu rakiya duk da ruwan saman da ake yi, bayan sun ɗauki hotuna cikin farin ciki da annashuwa. Daga cikin tawagar masu ziyarar sun haɗa da, M.Aminu Bukar, M.Musa Abba Zubairu, Nasiru Ibrahim Matazu, Sulaiman Sada Ƙerau, Isma’il Ibrahim Ƙanƙara, Lawal Tahir da Marwana Ibrahim Abukur. Gidan rediyon Companion FM dai yana yaɗa shire-shirensa kan Mita 104.5 a zangon FM a cikin garin Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here