Home Sashen Hausa Ghana: Anharbi mutum biyu a kusa da rumfar zaɓe

Ghana: Anharbi mutum biyu a kusa da rumfar zaɓe

An harbi mutum biyu a kusa da rumfar zaɓe

'Yan sandan Ghana

Mutum biyu sun jikkata sakamakon harbin bindiga a kusa da rumfar zaɓen Steps to Christ da ke mazaɓar Awutu Senya East.

‘Yan sanda sun ce wasu mutane ne da suka je wurin a baƙar mota suka buɗe wa wasu mutanen wuta a ƙaramar mota ƙirar KIA.

Rundunar ‘yan sandan Ghana ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an kai waɗanda aka raunata asibiti.

“An kai waɗanda ke cikin motar asibiti bayan sun ji rauni kuma ana ba su kulawa,” in ji ‘yan sandan, a cikin wata sanarwa.

“Ya zuwa yanzu ‘yan sanda na binciken duk wani zargin maguɗi da suka samu.”

Babu wani ƙarin bayani game da abin da ya jawo harbin. Rahotanni sun bayyana cewa an samu hatsaniya tun yayin aikin rajistar zaɓe a mazaɓar ta Awutu Senya East.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani

Zan Kashe Duk Wani Dan Siyasa Da Ya Fito Don Takara 2023- Sunday Igboho Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya yi gargadin...

Yajin aikin ‘yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya

Yajin aikin 'yan kasuwa ya tashi farashin kayan abinci a kudancin Najeriya Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka fara na ƙungiyar Amalgamated Union of...

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...
%d bloggers like this: