Advert

George Weah: Shugaban ƙasar da ake tura wa saƙonnin zagi da cin mutunci ta waya.

Shugaban Laberiya George Weah ya bayyana yadda ya samu tarin saƙonnin kar ta kwana na cin mutunci ta wayarsa daga mutanen da suke ikirarin cewa su magoya bayansa ne, waɗanda suke jin haushinsa kan ƙin taimaka musu

Shugaban ƙasar ya faɗi hakan yayin da ake wani taron wa’azi a coci.

Tsohon ɗan ƙwallon mai shekara 54 ya kusa kai wa rabin wa’adinsa a ofis kuma wasu na ƙorafin cewa gwamnatinsa ta gaza wajen samar da ayyukan yi wanda Mista Weah ya yi alƙawari a lokacin da yake takarar shugabancin ƙasa.

Wata jarida ta ruwaito shugaban ya shaida wa masu ibada a cocin cewa saƙo 999 daga cikin duk 1,000 da yake samu na zagi ne da cin zarafi.

Shugaban ya ayyana cewa ba zai taimaki duk wani mai zaginsa ko cin mutuncinsa ta hanyar aika masa saƙo ba.

”Kuna da girman kai kuma kuna tambayata wani abu, to ba zan yi ba. Ba zai yiwu kan neman taimako kuma kana raina shugaban ƙasa ba,” in ji Mista Weah.

Ya yi kaca-kaca da matasa ‘yan shekaru 19-20 da ke son su zauna su kaɗai maimakon zama tare da iyayensu.

“Ka san na yi shekara 18 ina barci a ƙasa? Me yasa kuke hanzarin rayuwa?” Ya tambaya.

Shugaban ya tashi ne daga kakarsa a wata unguwa da ke wani yanki a Monrovia, babban birnin kasar, daga nan ne ya zama tauraro kuma ya ci gaba da zama daya daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafar Afirka a kowane lokaci, inda ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Fifa a shekarar 1995.

Ya ce ya kamata matasa su riƙa tunanin yin kasuwanci ba wai su zauna da kansu ba.

“Wasun ku suna ce min in biya kuɗin hayarku; kuna da iyayenku kuma kuna neman in biya kuɗin hayarku; “Me yasa ba za ku iya rayuwa tare da iyayenku ba?

”Kudin da kake son biyan kudin hayarka; za ku iya amfani da shi tare da mahaifiyarku don kasuwanci?”

ko

Like this:

%d bloggers like this: