#RashinTsaro: Yadda wasu garuruwa fiye da ashirin a karamar hukumar Sabon-birni ta jihar Sokoto ke gudun hijira zuwa Jamhuriyar kasar Nijar wadansu kuma cikin garin birnin Sabon-birni.

Garuruwan sun hada da: Unguwar abzin, Garin Jari, Garin Gabas, Garin Kalage, da Garin Abara da wadansu kawo yanzu babu kowa a ciki sakamakon gudun hijira kan yawaita hare-haren yan bindiga a yankin.

Yankin karamar hukumar Sabon-birni dake gabacin jihar Sokoto na cigaba da tsundumawa cikin hadin matsin yan bindiga akai-akai tsakanin safe zuwa rana da cikin dare kullum.

Kawo yanzu mutanen garuruwa daban-daban ne ke gudun hijira zuwa Jamhuriyar kasar Nijar wasu kuma na tafiya a cikin garin birnin Sabon-birni don tseratar da ransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here