Advert
Home Sashen Hausa GARKUWA DA MUTANE: HABA GWAMNA BADARU

GARKUWA DA MUTANE: HABA GWAMNA BADARU

 

Daga Mansur Ahmed

Batun Garkuwa da mutane a Jigawa fa kullum abun girma yake yi kuma yanzu abin ya juya kan manyan ‘yan siyasa, yan kasuwa da ‘yan Kwangila, ya kamata Badaru ya hakura da yawon aikin Jam’iyyar APC, da zuwa Kasashen waje hutu da neman masu zuba hannun jari domin babu wadda zai zuba jari sai Kasa da Jiha sai akwai wadataccen zaman lafiya haka zalika ziyara wajen Buhari ma akai- akai a kyale ta a zauna a Jigawa.

A kira taro a tara masu ruwa da tsaki a Jihar nan tun daga kan Jami’a tsaro na kowanne rukuni a k’ara musu k’aimi a yaba musu ayi musu godiya a aikin da suke na tsare rayukan al’umma da namijin kokarin su dan suna iyakar kokarinsu kuma a nemi su sake rub’anya kokarinsu, a k’ira masu martaba Sarakunan Jihar nan su kira Hakimai, da Dagatai da masu Unguwanni da Hard’awa da wakilan kowanne rukuni na al’umma a sake jadadda musu amfani da muhimmancin zaman lafiya da hadin kai da bada labarin duk bak’uwar fuska da ake gani a cikin al’umma a kawo rahoto da wuri.

Sannan Mai girma Gwamna ya k’ira wadanda suke kwangilar bada Diesel da ake kunnawa fitilun kan titunan cikin garuruwa da hanyoyi ayi musu fad’a akan kashewa da ake yi da tsakiyar dare ko a bawa wani wajen a kashe wani wajen, a ja hankalin ma’aikatar da Works akan su gyara fitilun a Inda suke lalace

Sannan a k’ira Taron shugabannin kananan hukumomi a fad’a musu cewar a sake dawo da security meetings da ake yi a kananan hukumomi kuma ake kawowa rahoton kowanne sati gaban gwamna yana gani sannan a ware alawus mai tsoka ga mahalarta taron tattaunawar domin kowa yayi aikin da ya kamata ace yayi.

Allah ka k’ara zaunar da Jihar Jigawa lafiya, ka sa tafi kowacce Jiha zaman lafiya a Kasar nan, ka zaunar da Arewa da Najeriya lafiya alfarmar shugabanmu Annabi Muhammad S.A.W.

Shawara ce saura kuma wani gyaran Garayar yace adawar siyasa ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: