Wata ƙungiyar Mata zalla Masu sana’ar Downloading (Tura waƙoƙi da fina-finai ta Computer) a Katsina, Sun kai ziyara a gidan Sanata Sadiq Yar’Adua, da miƙa ƙoƙon barar su, akan Lallai suna neman ya fito Takarar Gwamnan jihar Katsina kuma sun Shirya tsaf domin mara masa baya.

Da take jawabi a madadin Masu sana’ar Downloading din Shugabar tace, a da sun janye ga duk wani Al’amari na Siyasa duba da halin da suka shiga, amma Jin cewa Sanata Sadiq Yar’Adua yana yinƙurin fitowa takara, tace basu ga ta zama ba duba da sun san wanene Sadiq Yar’Adua da irin ƙoƙarin sa. Don haka a madadin wannan ƙungiya suna goyon bayan sa ɗari bisa ɗari, kuma zasu shiga lungu da saƙo ganin sun jawo hankalin matan da sukayi fushi da al’amarin Siyasa saboda gazawar shugabannin baya.

Sanatan ya tofa Albarkacin bakinsa, inda ya ja hankalin Matan akan muhimmancin Alƙawari da kuma muhimmancin su a Siyasa, inda ya tabbatar masu da cewa Madamar ya samu Gwamnati zai maida hankalinsa a kan kyautata rayuwar su.

Taron ya gudana ne Ranara juma’a 31 ga watan Disamba a gidan Sanatan, dake GRA a cikin garin Katsina. Zamu kawo maku Bidiyon yanda taronnya gudana a Tashohin mu na sadarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here