Ganduje ya yi wa Kwankwaso ta’aziyya bisa rasuwar mahaifinsa

.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa rashin mahaifinsa, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.

Mahaifin Sanata Kwankwaso, wanda shi ne dagacin Madobi, ya rasu ne a daren Alhamis wayewar yana da shekara 93 a duniya.

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Muhammad Garba ya fitar, ya ce Gwamna Ganduje ya kaɗu da samun saƙon mutuwar, sannan za a dinga tuna marigayin da irin hikimarsa da dattako a matsayin na jagoran al’umma.

“A madadina da gwamnatin jihar Kano, ina yi wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Masarautar Ƙaraye ta’aziyyar wannan babban rashi.

“Haƙiƙa marigayin ya bar mana darussan koyo da suka haɗa da gaskiya da adalci da tsoron Allah a wannan jiha tamu,” in ji sanarwar.

Duk da cewa Gwamnan Ganduje da Sanata Kwankwaso ba sa ga maciji da juna saboda bambancin siyasa, wanda ya samo asali a lokacin rasuwar mahaifiyar Ganduje da Kwankwaso ya je ta’aziyya, akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Gandujen da mahaifin Kwankwason.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here