Guguwar sauyin sheƙar jam’iyyu na ci gaba da yiwa jam’iyyar APC mai mulki barna a Jihar Kano, inda shugaban ma’aikatan gwamna Abdullahi Ganduje na yanzu, Ali Haruna Makoda ya jagoranci wasu fitattun ƴan siyasa a Kano-ta-Arewa su ka fice daga jam’iyyar.

Da yake zantawa da DAILY NIGERIAN a daren jiya Juma’a, Makoda ya tabbatar da sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP ta Sanata Rabi’u Kwankwaso.

Ya ce tuni ya miƙa takardar murabus dinsa a matsayin shugaban ma’aikata ga Ganduje a jiya da rana.

Daga cikin wadanda suka sauya sheka daga APC zuwa NNPP akwai Badamasi Ayuba, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Dambatta/Makoda; Murtala Kore, dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Dambatta da; Abdullahi Wango, shugaban karamar hukumar Dambatta.

Sauran sun hada da Ahmed Speaker, mai binciken kuɗi na APC na Jiha; Najib Abdussalam, shugaban matasan APC na shiyyar; Umar Maitsidau, tsohon shugaban karamar hukumar Makoda; Halliru Danga Maigari, tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar Rimingado/Tofa da; Hafizu Sani Maidaji, tsohon dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Dambatta.

Sauran wadanda suka bi ayarin sauya sheƙar akwai Safiyanu Harbau, tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Tsanyawa/Kunchi, Habiba Yandalla, tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar APC, da wasu fitattun ƴan siyasa.

Tunti tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Kano kuma ɗan majalisar wakilai mai ci, Alhassan Rurum tare da tsohon mai baiwa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shawara kan majalisun taraiya, Kawu Sumaila suma su ka koma NNPP.

Hakazalika ƴan majalisar dokokin ka Kano da ga jam’iyun APC da PDP sama da goma sha huɗu ne su ka sauya sheka zuwa NNPP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here